Thursday, November 29, 2018

Yadda matan Nigeriya Suke shan wahala a Nigeria


Wasu mata 'yan Najeriya da suka tsinci kansu a
Jamhuriyar Nijar bayan sun bar gida da zummar
tafiya kasar Saudiyya sun koka kan irin halin
ha'u'la'in da suka samu kansu a ciki.
Matan dai na yawon neman ayyukan cikin gidaje
kamar wanki da shara da sauransu, ba tare da an
biya su hakkinsu yadda ya kamata ba.
WakiliyarmuTchima Illa Issoufou ta ziyarci daya
daga cikin matan Zainab a gidan da take aiki,
wacce ta shaida mata cewa ta bar Najeriya ne
zuwa Nijar da zummar za a kai su aiki Saudiyya,
amma kuma a yanzu ba su ga tsuntsu, ba su ga
tarko.
"Na farko dai an kawo mu wajen da aka ce ta nan
ake tafiya Saudiyya, sai kuma daga bisani aka ce
mana an rufe, mu tafi idan an samu lokaci za a
daidaita komai.
"Daga baya kuma aka ce ba za a daidaita ba, kowa
ya je ya samu gidan aiki don rufawa kai asiri," in ji
Zainab.
'Mun sha bakar wahala'
Zainab ta shaida wa BBC cewa a sakamakon rashin
tudun dafawa a kasar da ba tasu ba, ya sa suka
shiga gararambar neman aiki ba dare ba rana don
tallafawa kansu.
"Mun sha wahala sosai domin kafin na samu gidan
da nake aiki yanzu, unguwa daidai ne ban sani ba a
Yamai, wata unguwar ma idan muka je sai mu
bata.
"Kuma duk yawon neman abin da za mu taimaki
kanmu muke, amma a hakan ma ba biyan bukata
yadda muke so. Wata ma sai ka gama yi mata aiki
sai ta baka abin da bai fi naira 100 ba. Wallahi har
kuka muke yi."
Asara
"Ni dai ban shirya komawa gida ba a yanzu tsakani
da Allah, saboda ba zan koma na ga takaici ba
sakamakon sayar da duk abin da na mallaka don
na yi wannan tafiya," a cewar Zainab.
Ta ci gaba da cewa a don haka ne ta dage neman
na kanta a Nijar duk da ba ta samu zuwa
Saudiyyan ba, inda aka lasa mata zuma a baki
cewar za ta mayar da abin da ta kashe a
kankanin lokaci.
"Don haka gara na zauna a nan da wuya da dadi
har na hada dan wani abin kirki."Mata na tafiye-
tafiye zuwa Saudiyya da wasu manyan kasashen
duniya ne don neman karuwar arziki a can.
Sai dai da yawansu ba sa iya cimma wannan burin
nasu, inda da dama daga cikinsu suke bigewa da
karuwanci da mu'ammali da miyagun kwayoyi da
kuma barace-barace.

No comments:

Post a Comment