Friday, November 30, 2018

FA'IDODIN DAKE CIKIN YIN AURE


Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu Kididdigu ba.
Amma ga wasu ka'dan daga ciki zamu lissafo
kamar haka:
1. Yin aure biyayya ne ga umurnin Allah da
Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (saww) farin
ciki aranar lahira. Yace : "Kuyi aure ku hayayyafa.
Domin ni zanyi ma sauran al'ummomi alfahari daku
aranar Alkiyamah".
3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito ta
jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! "LA
ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI.
4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da zasu yi
maka addu'a bayan rasuwarka. Wannan yana daga
cikin ayyukan da ladansu ba zai yanke ba har
abada.
5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun
mutum daga kalle kallen Haramun, sannan ya kare
masa al'aurarsa daga Zina.
6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar taimaka ma
'Yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta
kenan daga Zina.
7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da
ninkawar ladanka fiye da wanda bashi da aure.
8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan ciyarwa da
Matarka, da daukar nauyinta, da ladan samar
mata da Mazaunin da zata rayu.
9. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Qara yawan
Musulman duniya ta hanyar haihuwar da zaka
samu.
10. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Karkatar
da himmarka daga kan neman biyan bukatarka ta
hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma
samun ladan saduwa da iyalanka.
11. Zaka samu lada mai girma sosai idan Har Allah
ya azurtaka da 'Ya'ya mata guda biyu, kumq kayi
hakuri dasu ka kyautata musu, ka kyautata
tarbiyyarsu, Su zasu zama Garkuwarka daga shiga
wuta.
12. Idan kuma har 'Ya'yanka guda biyu suka rasu,
kuma kayi hakuri, to Allah zai shigar dakai Aljannah
saboda wannan.
13. Ta dalilin aure zaka samu Qaruwar mutuncinka
da darajarka acikin al'ummah. Ka shiga sahun
mutanen da zasu iya jagorantar lamuran rayuwar
al'ummah.
14. Ta dalilin aure ne zaka Samu Taimakon Allah
cikin al'amarinka. Kamar yadda Manzon Allah
(saww) yake cewa: "MUTUM UKU, HAKKI NE AKAN
ALLAH YA TAIMAKESU
(a) WANDA ZAI YI AURE DON NUFIN KAME MUTUNCINSA.
(b). BAWA WANDA YAKE NEMAN 'YANCINSA SABODA YA
SAMU DAIDAITUWA (ACIKIN ADDINI)
(c). MUJAHIDI (MAI YAKI DON DAUKAKA ADDININ ALLAH).
15. Ta dalilin aure ne zaka samu Qaruwar yawan
dangi. Domin duk mutanen da ka auri 'yarsu ko
Qanwarsu, to ka zama nasu.
16. Ta dalilin aure ne zaka samu zuriyya tsarkaka
wadanda zasu bauta ma Allah kuma za'a baka
ladan dukkan aikin ibadar da sukayi.
* ZAUREN FIQHU yana kira ga Matasan da suke da
ikon yin aure, lallai aje ayi aure. arage burin duniya.
Kullum rayuwa tafiya take yi.

No comments:

Post a Comment