Friday, November 30, 2018

Yadda ake wankan janabaa



Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.
Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai
'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira
'siffatu kamal' (ta kamala).
Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan
kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka.
Farkon abin da zaka fara yi shi ne:
zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke
hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a
cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka، a dai-
dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka
kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda
yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi
tsarki kenan ، to daga nan kuma sai kayi alwala
irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake
a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne
wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi
shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda
biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai
ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya
bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga
jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam
yakan bude musammam gashin sa na ka, idan ka
zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai
ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a
cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka
tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata
na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka
na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka.
To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game
dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da
bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na
hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina. To idan
kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne
sai ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta
hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro.
Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba.
In wankan janaba ne haka zakayi, in na haila ne haka
za'ayi inma wanka ne na biki haka mace zata yi,
idan wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi
ma haka zaka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.
Idan mutum zai yi siffa ta 'Al ijza' wadda ta
wadatar ba sai kayi alawa acikin ta ba, kana zuwa
kayi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan
ka watsa a jikin ka ya game ko'ina, inma wani
kududdufi ne ko rami ko swimming pool sai kayi
tsalle ka fada aciki, dama ka kulla niyyar ka kafin
ka shiga, daga ka fito abin da zakayi shi ne
abubuwa guda biyu, kurkurar baki da kuma shaka
ruwa a hanci da facewa.
Shike nan, kuma ya halatta kayi sallah da wannan
wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika kamala
saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar
kamala, ya fika lada.
Kasancewar ba'ayi alwala ba ciki, wannan ka'idace
ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR)
idan sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to
da ka kawar da babban kari, karamin ma ya tafi.
Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin ace
babban ma ya tafi.
Bissalam

No comments:

Post a Comment