Friday, November 30, 2018

Maganin Ciwon Suga da Hawan Jini

Ko ka san cewa masana ilimin kimiyyar magunguna
na Kasar Sin da India sun tabbatar da cewar daya
daga cikin manyan magungunan warkar da ciwon
suga (diabetes) shine ganyen mangwaro?
Ganyen magwaro na dauke da sinadarai masu
yawan gaske da ke amfana wa jikin Dan’adam,
amma kash! Mutane da dama basu sani ba.
Yadda ake amfani da shi a matsayin maganin cutar
suga ( Diabetes)
(1) ka tsinko ganyan mangwaronka masu kyau sai
ka wanke su sosai
(2) Ka sanya ruwa a murhu ka tafasashi har na
tsawon minti biyar ba tare da ganyen ba.
(3) Sai a zuba ganyen a cikin ruwan zafin da ke kan
murhu tare da OLIVE oil wato man Zaitun, a barshi
yayi ta tafasa har na tsawon mintuna biyar zuwa
goma.
(4) Sai a sauke shi a tace
(5) Sai a sanya shi cikin kwano ko gilashi mai kyau
a barshi ya kwana
(6) Sai a sha wannan ruwan da sassafe bayan ka
tashi daga barci, kafin ka ci komai.
Wannan maganin, yana kawar da abubuwa marasa
kyau masu guba daga jikin mutum, kuma yana rage
yawan suga da ke cikin jini. Yana kuma saukar da
hawanjini sosai.
Haka kuma yana taimakawa matuka wajen
kwantar da tari, ASTHMA, yakan sa ka samu
numfashi mai kyau mai sauki.
Zaman dar-dar ko rashin nutsuwa sosai
(restlessness), Idan ka zuba cokali biyu ko uku a
cikin ruwan wankan ka, sannan kayi wanka dashi,
yana sanya kaji jikinka garau kuma kaji hankalin ka
ya kwanta soasai.
Dutsen dake cikin hanta ko Madata ko Koda (wato
kidney stone), mai wannan ciwon zai iya busar da
ganyen mangwaro a inuwa sannan a daka shi a
zuba garin acikin kofi/glass ko kwano a barshi ya
kwana a rinka sha kullum da safe. Wannan yana
narkar da dutsen dake jikin koda sosai.
Tari da Gushewar Murya ko Asthma ko Murya ,
A dafa ganyen Mangwaro a sanya masa Zuma
kadan yana taimakawa kwarai da gaske cikin
sauri.
> Attini ko kashi da jinni; Sai a shanya ganyen a
inuwa a busar dashi a mayar dashi gari, a rinka
sha sau uku a rana . Yana tsayar da wannan
cutar.
> Ciwon Kunne; Idan aka tatse ruwan ganyen
mangwaro aka dan dafa shi, sai a rinka digawa a
cikin kunnen. Wannan na maganin ciwon kunne.
Kunar Wuta
Sai a kona ganyen mangwaro har ya zama toka, sai
a rinka barbadawa a wurin da aka kone, yana
warkar da kunar cikin sauri zai bushe In Sha-
Allahu.
Shakuwa da ciwon makogoro
Idan kana shakuwa ko zafin makogwaro. Sai ka
kona ganyen mangwaro ka shaki hayakin, yana
maganin tsayar da shakuwan da kuma ciwon
makogwaro.
Ciwon ciki
Idan kana yawan ciwon ciki sai ka sanya ganyen
mangwaro a cikin ruwan dimi ka barshi ya kwana
sannan ka sha da safe kafin kaci komai. In ka juri
yin hakan zai warkar maka da ciwon ciki kowane
iri ne in Allah Ya yarda.
Shan ganyen mangwaro a kai a kai yana kuma kara
inganta garkuwan jiki kuma yana maganin hana
kumburin ciki. Yana da kyau ka jurewa shan
wannan ganyen mangwaro a duk safiya domin ganin
yadda suga dake cikin jikin ka zai sauka cikin sauri.
Allah (SWT) yasa mudace.

No comments:

Post a Comment