Thursday, November 29, 2018

Jam’iyyar APC Ta Dirar Wa PDP Da Atiku


Jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da sanya
siyasa a kan kashe sojojin Nijeriya daka yi a harin
da ‘yan Boko Haram suka kai garin Melete.
Jam’iyyar mai mulki ta kuma ce, zargin da
jam’iyyar adawa ke yin a cewa, an karkatar da
kudaden yaki da ta’addanci zuwa harkar yakin
neman zaben 2019, wani abu ne dake kai ga tuna
mana zamani mumamuna da jam’iyyar PDP ta yi
a lokacin tana mulki.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne a sanarwa da
jami’in watsa labaranta, Mallam Lanre Issa-
Onilu, ya raba wa manema labarai a Abuja ranar
Talata.
Sanarwar da aka raba ya nuna cewa, “Muna yin
tir da abin da muka gada daga gamnatin da ta
wuce na yadda jam’iyyar PDP ta kwashe dukkan
kudaden da aka ware don yaki da ta’adanci a
yankin arewa maso gabas.
“A bayyana yake cewa, dan takarar jam’iyyar PDP,
Alhaji Atiku Abubakar, ya shirya amfani da harkar
mutuwar sojojinmu a harin da aka kai musu a
sansanin sojoji na Metele.
“Jam’iyyar PDP da Atiku na neman siyasantar da
lamarin mutuwar ‘yan kasa da suka mutu suna
kare kasar daga ‘yan Boko Haram, abin da suka yi
rashin imani ne ga sojojin da suka mutu da kuma
iyalansu.”
APC ta kuma kara da cewa, dama haka halin
jam’iyyar PDP yake, na amfani da halin da kasa ke
ciki wajen neman farin jinin siyasa, kuma za su
girbi abin da suke shukawa lokacin zabe dake
tafe.
Sanarwa ta kuma kara da cewa, “Yan Nijeriya na
sane cewa, PDP na neman samun farin jinin da ba
su da shi ne, kuma lallai za su ji kunya nan gaba
kadan
“A yayin da jam’iyyar APC take zaman jajen
mutuwar jami’an tsaronmu da suka rasa
rayukansu a bakin aiki muna kuma ci gaba da
jinjina musu a kan aikin kare kasa da suke yi.
“Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na
nan akan bakansu na ganin an kawo karshen
wannan tashin hankalin tare da tsugunar da
wadanda aka tarwastsa sakamakon yakin.”

No comments:

Post a Comment