Friday, November 30, 2018

Bambanci Tsakanin Maniyyi, Maziyyi Da Kuma Wadiyyii


Bambanci Tsakanin Maniyyi, Maziyyi Da Kuma
Wadiyyi
...yada wannan rubutu nada muhimmanci domin
karuwar al'ummar musulmi
A kwai sakonni da dama daga 'Yan uwa da suka yi
tambaya (wata tambayar ma tafi wata guda)
akan bambancin wadannan ruwaye. Hakan ya nuna
kishinsu ga addini wanda ya sa muka yi tunanin
sanyawa a fili wadanda ba su tambaya ba ma su
amfana. Na dade ina tunanin sawa dan sauwakewa
kaina amsa tambayoyi daya bayan daya.Amma ina
jin nauyi wajen bada amsa ya sa na kasa, yau da
aka kuma yi mini tambayar na ga ya dace in sanya
tunda;
"INNALAAHA LA YASTAHYI MINAL HAQ.
Nana A'isha tana cewa:
"Allah ya jikan MATAN MADINA ko kadan KUNYA bai
taba hana su neman sanin addininsu ba" Idan muka
ce za mu ci gaba da jin nauyin tambaya ko bada
amsa saboda kunya, to zamu rayu cikin jahilci,
wanda wannan ba uzuri bane a wurin Allah.
Dan haka ga banbancin dake tsakaninsu:
{1}. MANIYYI
==========
Maniyyin namiji:- Ruwa ne mai kauri FARI wanda
yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa,
ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin
da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin
hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe
yana kamshin kwai.
{1A}. MANIYYIN MACE:- Ruwa ne TSINKAKKE, MAI
FATSI-FATSI, wani lokacin kuma yana zuwa FARI,
wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar
saduwa, ko wasa da farji.
Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa,
za ta ji tsananin sha'awa da dadi lokacin
fitowarsa. Kuma warinsa yana kama da warin
hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe
shima yana kamshin kwai. Sannan sha'awarta za
ta yanke bayan fitowarsa.
HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine:- YANA WAJABTA
WANKA.
{2}. MAZIYYI:
==========
Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar
sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce
kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin
da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin
wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya
tafiyar da sha'awa, kuma wani lokacin ba a sanin
ya fito. Malamai suna cewa:- Maziyyi ya fi fitowa
mata, fiye da maza.
HUKUNCINSA SHINE:- A WANKE FARJI GABA DAYA, DA
KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA.
{3}. WADIYYI
==========
Wani ruwa ne mai KAURI da yake fitowa a karshen
fitsari, ko kuma karshen ba haya ga wanda ya jima
bai yi jima'i ba, yana fitowa ga wadanda ba su da
aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu
ta aure, ina nufin namiji ko mace.
YANA DAUKAR HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI.
Allah shine ma sani.

No comments:

Post a Comment