Thursday, November 29, 2018

An Bukaci Gwamnati Ta Tallafa Wa Bangaren Ilimi


Lokaci ya yi da gwamnatocin kasar nan tare da
al’umma musamman masu hali da su kara hada
hannu wajen ganin matasa sun samu ilimi mai
kyau da inganci, kasashen da suka sai da suka
mayar da hankulan su wajen samarwa da
al’ummar su sannan suka kai halin da ake ganin
sun kai ta fannin cigaban azamani tare da bayar
da fifiko wajen samarwa matasa ilimi.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin babban
Manajan Daraktan Kamfanin sufurin motoci na AI
Gizna Global Oil and Transport Sebices Limited,
dake Kano, Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu ,
alokacin da yake zantawa da manema labarai a
Kano.Maharazu Ibrahim ya kara a cewa idon
al’ummar kasar nan musamman matasa suka
samu ilimi a su zamanto masu basira da kaifin
hankali tare kuma da tunani mai kyau da za su
zamanto abin alfahari da kawo cigaba ga
al’ummar kasa baki daya,
Manajan daraktan na AI Gizna ya nuna damuwar
shi game da yadda matasa na arewacin kasar
nan aka bar su abaya a harkokin ilimi da koyon
sana’oi, idon ka kwatanta su da matasan
kudoncin kasar nan . A cewar shi da yawa daga
cikin matasan arewacin kasar nan suna sako
sako wajen neman ilimin zamani da koyon
sana’oin dogaro da kai , wannan na daya daga cikin
yadda wasu ke amfani da su wajen tayar da
rigingimun siyasa dona addini da sauransu ,
sabodahaka ya zama wajibi al’umma su hankalta
, matukar aka baiwa matasan ilimi da sana’oi ba
za su amince wani ko wasu su yi amfani da su
ba wajen tayar da hargitsi ba .
Ganin ana kara tunkaran zabubbukan kasar nan
na 2019 ya jawo hankulan matasan da cewa ka
da su yarda a bari ayi amfani da su wajen tayar
da rigima alokacin yakin neman zabe da kuma
ranar zabe har ya zuwa ranar sanar da
sakamakon zaben shugaban kasa , gwamna, da
sauransu inji matashin dankasuwa.
Iyaye kuma su tabbatar sun rika kula da zirga
zirgan yaran su tare da sanin abokan huldarsu
da taimakawa ilimin su da tarbiyarsu da sauran
abin da ya rataya iyaye su yi wa yaran su.
A matsayin shi na manajan daraktan sufurin
motoci na AI Gizna ya yi kira ga gwamnati da ta
kara himma wajen gyara hanyoyin kasar nan da
motoci ke bi domin zirga zirga, rashin gyaran na
barazana da harkokin sufuri da wasu lokutan ke
janyo asarar rayuka da dukiyoyin masu harkar
sufuri da matafiya, amma ya ya ba da yadda
gwamnatin ke kokarin gyara wasu manyan
hanyoyin motoci na kasar nan musamman daga
Kano, Kaduna, zuwa Abuja.
Daga karshe Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu, ya
shawarci direbobin kasar nan da su guji tukin
ganganci da hakan ke jawo asarar rayuka da
dukiyoyin al’umma, sannan kuma har ila yau
direbobin su sanya tsoron Allah tare da rike
amana da masu motoci suka ba su , abin bakin
ciki ne da wasu direbobin ke aikata rashin
gaskiya da iyayen gidon su watau masu motocin
sufuri.

No comments:

Post a Comment