Thursday, November 29, 2018

Atiku Shi Zai Dau Ragamar Nijeriya Da Zimma –Obasanjo


Tsohon Shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo
ya ce, tsohon mataimakin sa, kuma dan takaran
shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar,
zai dauki duk wani nauyi da za a dora mas da
himma.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wajen nadin
Sarautar Atiku Abubakar, a matsayin Wazirin
Adamawa, wanda Lamidon Adamawa, Dakta
Mustapha Barkindo, ya yi a fadar sa.
Ya ce, “A lokacin da muke tafiyar da al’amurran
gwamnati tare a Abuja, sam ba ya wasa da duk
wani abu da ya shafi al’ada. Kai mutum ne da
baya wasa da al’adar mutanan sa. Duk aikin da
aka dora maka a kasa ko ma a duk duniya, ina da
tabbacin z aka dauke shi ne da himma.”
A na shi jawabin, Atiku cewa ya yi, zai bayar da
mahimmanci ga sashen Masarautun mu na
gargajiya a kasar nan, ta hanyar daukaka su da
matsayin su a duniya.
Ya ce, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ciyar da
Masarautar Adamawa gaba da ma Masarautun
gargajiya na kasar nan baki-dayan su.
Atiku, wanda ya rika kiran Obasanjo a wajen
taron da shugabana, ya godewa tsohon Shugaban
kasan a bisa gudummawa da kulawan da yake yi
ma shi.
Atiku, ya nuna farin ciki da jin dadin sa da
Sarautar Waziri da aka nada ma sa, wanda hakan
yana nufin shi ne na biyu a Masarautar ta
Adamawa.
“Mai Martaba ya ba ni Sarauta mafi girman
matsayi a kan kowacce a bisa irin ci gaban da na
kawo. Marigayi Lamidon Adamawa, Aliyu
Mustapha, Allah Ya jikansa, shi ne ya nada ni a
matsayin Turakin Adamawa, a lokacin ina dan
shekaru 35, ya kuma shigar da ni a cikin ‘yan
Majalisar sa. A matsayin ka na wanda ya gaje
shi, ga shi a yau ka maishe ni mutum na biyu a
wannan Masarautar, wanda na karba tare da jin
dadi da farin ciki gami da dukkanin girmamawa a
nadin da ka yi mani a matsayin Wazirin
Adamawa.
Lamidon na Adamawa ya ce, an yi wa Atiku nadin
ne a bisa irin ci gaba da kuma gudummawar da
yake baiwa Nijeriya da kuma Masarautar ta
Adamawa musamman.
“Hakanan Atiku ya bayar da gudummawa wajen
samar da hadin kai a tsakanin al’ummar na
Adamawa, da kuma bayar da shawarwari masu
kyau ga Masarautar ta Adamawa,” in ji Lamido.
Barkindo, ya shawarci sauran masu rike da
Sarautu a Masarautar da su hada kai da sabon
Wazirin na Adamawa.
Baya ga Obasanjo, sauran manyan bakin da suka
halarci bikin nadin sun hada da, tsohon Shugaban
kasar nan, Goodluck Jonathan; Shugaban Majalisar
Dattawa, Dakta Bukola Saraki; Kakakin Majalisar
Wakilai ta kasa, Yakubu Dogara da wasu
Gwamnonin Jam’iyyar PDP da suka hada da,
Ibrahim Dankwambo (Gombe); Darius Isiaku
( Taraba); Abdufatah Ahmed ( Kwara); Seriake
Dickson (Bayelsa); Udom Emmanuel ( Akwa Ibom)
da Aminu Tambuwal (Sakkwato).
Tsaffin gwamnonin da suka halarci bikin sun hada
da, Attahiru Bafarawa na Jihar Sakkwato; Rabiu
Kwankwanso (Kano), da Boni Haruna, (Adamawa),
bikin kuma ya sami halartar ‘Yan Majalisun
tarayya na Jihohi na da, da kuma masu ci a halin
yanzun da dama.

No comments:

Post a Comment