Friday, November 30, 2018

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH GUD (91)


Hadithi daga Thabitu bn Ajlan daga Alqasim bn
Muhammad daga Abu Umamah (rta) yace Manzon
Allah (saww) yana cewa :
"IDAN RANA TA FITO DAGA MAFITARTA KAMAR SIFFARTA
NA LOKACIN LA'ASAR SANDA TAKE FADUWA A
MAFADARTA, SAI MUTUM YA SALLACI RAKA'A BIYU DA
SUJADU GUDA HUDU, TO ZA'A RUBUTA MASA LADAN
WANNAN WUNIN KUMA A KANKARE MASA KUSAKURENSA
DA ZUNUBANSA. KUMA IDAN YA MUTU AWANNAN RANAR
ZAI SHIGA ALJANNAH".
ADUBA :
Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy (Juzu'i na 8 shafi
na 192).
QARIN BAYANI
***************
Wannan lokacin da ake nufi acikin wannan hadisin
shine lokacin hantsi. Domin shine ka'dai lokacin da
yayi kama da lokacin faduwar rana.
Hakika sallar walaha teana da lada mai yawa.
Manzon Allah (saww) ya fadi falalarta acikin
hadisai masu yawa.
Har ma akwai hadisin dake nuna cewa duk wanda
ya sallaci walaha ladansa kamar na wanda yayi
sadaqah ne sau 360.
Allah yasa mu dace da samun wannan babbar
falala. Ameen. Zaka iya yinta kafin ka tafi wajen
aiki ko kasuwarka. Tun daga karfe 7:30 har zuwa
11:45 duk lokacin Walaha ne. Hasali ma lokacinnata
yafi haka fa'di.
Allah yasa mu dace ameen.

No comments:

Post a Comment