Thursday, November 29, 2018

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga ’Yan Kungiyar Boko Haram


Na rubuto muku wannan wasika ne saboda nasan
zata isa inda ku ke, kuma sakona inada tabbacin
zai yi tasiri matuka a gurinu. Ya ku ‘yan barandan
kungiyar fafutukar kafa gwamnatin Musulunci
wannan fili mai taken HANGEN NESA yana
tattaunawa ne akan matsalolin da suka addabi
wannan kasar, musamman bangaren siyasa,
kasuwanci da kuma tsaro. Matsayina na
marubucin shafin Mailafiya, na ga ya dace in
rubuto muku wannan budaddiyar wasika, domin
in kara tunasar daku halin da hare-haren ku
yake jefa al’ummar kasar nan, da kuma yadda
kuka sanya musulmai cikin zulumi da kuma yadda
ake daukansu matsayin ‘yan ta’adda.
Ya ku ‘yan Boko Haram (kamar yadda akafi gaya
muku) kusani duk wani bincike da ilimi na
Musulunci babu inda ya ce ayi jihadi ta hanyar
kashe wadanda suka karbi addinin Allah, suna
sallah, suna azumi, suna kuma duk wata ibadar
da addini ya halasta, babu inda Allah yayi umarni
da ayi yankan rago ko kisa ga abokan zama
wadanda basu karbi sakon ba, saboda haka ne ma
ya aiko Annabawa, ya kuma sanya musu hikima
ta zance da basu littafi amatsayin wanda zai
nuna aikin da suka zo yi ban kasa, da ana kashe
al’umma hakanan, da an aiko malaku tunda wuri
sun karkashe mutanen Annabi Nuhu (A. S) amma
saboda shi Addinin Allah yana son zaman lafiya da
kwanciyar hankali, sai ya ce ayi kira zuwa addinin
gaskiya, wannan shi ne babban jihadin da Addinin
Allah ya amince, duk da ni dalibin ilimi ne, amma
kai tsaye zan iya cewa abinda ku ke ba shi ne
ainihin jihadi da Addinin Musulunci ya yi koyi ba.
Wannan kenan.
Ya ku wadannan mutane, kun yi amfani da sunan
Musulunci, kun kashe rayukan da ba za su kirgu
ba, kun kashe mutane suna Sallah, kun kashe
mutane suna tafiya zuwa guraren sana’ar su ko
makaranta, na dauka idan Addinin Allah ku ke
karewa, bazaku kashe ‘yan uwanku ahalin bautar
Allah ba, kuma Ubangijin da kuma kuka yadda
dashi, kuma ku ke da’awar yin jihadi don daukaka
Addinininsa. Shin kunada masaniyar cewar kun
maida mataye zawarawa, kun maida yara
marayu, kun maida gidaje kufe, kun sanya
hawayen mu yafara kafewa saboda yawan
zubewa da yake, kun kashe dakarun kasa dake
kare al’ummar kasa ? Don Allah wannan wace
iriyar jihadi ce ku ke yi, wace iriyar littafin Addini
ku ke karantawa wanda yake umartar ku dakuyi
wannan aikin ?
Amatsayina da dan kasa, mai kishinta da kuma
kokarin komai ya tafi daidai, ina amfani da
wannan damar da nike da ita ta isar da sako. Ina
kiranku da ku ji tsoron Allan daya halicceku, ku ji
tsoron haduwa da Ubangijin daya halicceku,
wanda zai yi hisabi akan duk ran da kuka kashe,
ku ji tausayin al’ummar da ku ke kassarawa, ku ji
tausayin musulmai da ake hantarar su saboda
ku, ana cewa su ‘yan ta’adda ne, ku yadda ayi
maslaha tare da ajje makaman ku tun kafin a
karar daku, sojojin mu masu tarin yawa da kuka
kashe, mutanen da ku ka kama ku ke azabtarwa,
‘yar uwarmu da ku ka kashe (Hauwa Liman)
kwanakin nan za su sanya gwamnati takara
daukan wasu matakan gaggawa akanku, ku ji
tsoron Allah ku fadi wadanda ke daukar
nauyinku, ku ji tsoron Allah ku tsayar da ayyukan
kashe al’umar da ba su ji ba, kuma basu ganiba,
amma kun kashe ahalinsu, danginsu kuma kun
rabasu da gidajen su da garuruwan su.
Ya ku ‘yan boko haram, mun sani cewar akwai
wasu makiyan kasa da suke amfani daku, kuma
suna daukar nauyin ku, munsan cewa kayan da ku
ke aiki dasu kuna daukan rayukan al’umma, lalle
akwai wasu ‘yan siyasa, turawa da masu kudi da
suka san wannan ta’asar da ku ke, kuma suke
temaka muku, saboda basusan kasancewar
NIJERIYA dunkulalliyar kasa, tashin hankali da
rashin zaman lafiya sune ababen sonsu, ku ji
tsoron Allah ku fallasa su. Ina kira agareku da
kuka kara karanta zancen ubangiji (Alkur’ani mai
girma ) na tabbata zaku gane cewar abinda ku
ke aikatawa yayi hannun riga da sakon Ubangiji,
na tabbata za ku yi dana sani da zubar da
hawaye bisa wannan ta’asar da kuka aikata,
kuma ku ke kan aikatawa.
Ina kara kiranku da cewar ku ajje makaman ku,
kubar wannan bakar sana’ar ta daukan rayukan
al’umma. Saboda biyayya da kauna da Addinina ya
sanya dole

No comments:

Post a Comment