Thursday, November 29, 2018

Amfanin Kunun Aya ajikin Dan-adam

Aya wacce muka sani a kasar Hausa, ana kiranta
da tigernut a harshen Turanci, Yarabawa na
kiranta da suna Ofio, a yayin da su kuma kabilar
Igbo suke kiranta da suna imumu ko aki.
Ana samun aya a sassa daban-daban a kasashen
duniya ciki har da Nijeriya.
A can baya, an dauki aya tamkar kayan kwalama
ne kawai wanda yara ke ci dan jin zaki ga bakinsu
wanda ya sa har dakuwar ayar ake yi ana
siyarwa. Wannan baya rasa nasaba da rashin
samun cikakken bayanin alfanun aya. Daga bisani
sai kimiyya ta bankado binciken wasu masana a
kan dimbin amfanin aya wanda jin haka ya sa har
kunun aya ake yi a yanzu.
Sai dai kuma har zuwa yanzu akwai mutane da
dama da ba su san amfanin shan kunun aya ba,
inda wasu sun dauka abin sha ne kawai maganin
yunwa ko kayan marmari, wasu kuma kayan zaki
suka dauke shi.
Ganin haka ya sa na zo maku da bayani tiryan-
tiryan kan aya da kuma amfaninta.
Aya tana kumshe da wasu muhimman sinadirrai
na musamman dake gina jiki, masu inganta
lafiyar jinin jiki da tsokar gangar jikin dan’adam,
masu kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin
cuta, masu maganin wasu illoli da matsalolin da
ke damun maza da mata da makamantan su.
Kadan daga cikin wadannan sinadiran sun hada da
: Phosphorus, bit E, Fat, protein, dietry fibre,
potassium, zinc, sodium, calcium, magnesium,
copper, bit C, da carbohydrates.
-An yi amanna cewa aya tana sanya jini kai wa
da karuwa a cikin kowane lungu da sako na jiyojin
jiki wanda a dalilin haka ya sa ake ganin tana
karin shawa da karfin zakari ga namiji, domin
jiyojin zakari za su rinka samun jini wadatacce
da zai rinka kai wa da kawo wa.
-Aya tana samar wa jiki da wadataccen sinadirin
bitamin E da bitamin C da kuma Zinc da sinadirin
kuercetin wanda suke da matukar amfani ga
mace ko namiji musamman masu neman
haihuwa.
-Aya tana kara yawan ruwan maniyi da kuma
lafiyarsa ga namijin da ruwan maniyinsa suka ja
baya ko yake fama da karamcin ‘ya’yan maniyi a
jiki.
-Aya tana karawa mata ni’ima, sai a nemi ayar
misalin gongonin madara daya da kuma garin
dabino rabin gongoni sai a hada da ciyawa nan da
ake kira dan hakin daka raina sai a dake a maida
ta dakuwa ko a maida su tamkar alawa a dunga
ci, kada a saka suga ko kadan.
-Aya tana kara yawan ruwan maniyi ga namiji
sai a nemi garin aya gongoni daya sai a sanya
ruwan kwakwa a dame garin a dunga sha.
-Aya na samar da yawan oestrogen wanda
karamcinsa na haifar da rashin haihuwa ga mata.
-Aya na samar da testosterone wanda shi ne
ida ya karamta ga jikin namiji to zai kasance
baya da shawa tamkar bai balaga ba, zai ga yana
ramewa kuma zakarinsa baya karuwa haka
kuma zai kasance baya da maniyi lafiyayye wanda
wannan zai hana shi haihuwa.
-Mata da kuma mazan da suke da kalubale na
rashin samun haihuwa sai su rinka amfani da aya
akai-akai.
-Aya na kara yawan ruwan nono. Dan haka ga
duk macen dake shayarwa sai ta rinka amfani da
kunun aya akai-akai bayan taci abinci.
-Mazan dake neman amfanuwa da aya sai a
zanka hada garinta dana citta a nike sai sun
koma gari sai a sanya babban cokali biyu a cikin
zuma a sha.
-Idan an ci abinci to sai a nemi kofi daya na
kunun aya a sha, hakan zai taimakawa ciki dan
saurin narkar da abinci.
-Idan aka hada garin tafarnuwa dana citta da
garin aya aka dama a tare da zuma zai bada
wasu magungunnan na daban wadanda za muyi
bayaninsu nan zuwa gaba.
-Mai fama da bayan gari mai tauri kamar na
dabbobi to sai ya rage cin shinkafa da abinci mai
karfi sai ya lazamci shan diyan itatuwa daga
bisani ya biyo baya da shan kunun aya.
-Kada a sanya suga a cikin kunun aya.
-Kada a tafasa kunun aya.
-Za a iya hada kwakwa ko dabino a madadin
suga.
Amfanin Nonon Rakumi A Cikin Dan’adam
A shekarrun baya,mutane na daukar nonon
rakumi a matsayin abinci ga diyan rakumman ko
ga masu kiwon rakumma kawai. Sannu a hankali
sai ga bincike ta bangaren magunguna sun kai ga
gano alfanun nonon rakumi.
Akwai wani lokaci a zamanin Manzon Allah
(S.A.W) da wasu mutane suka je Madina sai
rashin lafiya ta kamasu mai nasaba da
cututtukan ciki sai Manzon Allah (S.A.W) ya
umurcesu da su gauraya nonon rakumi da
fitsarinsa sannan su sha. Suna sha nan take sai
suka warke.
Wannan wani dalili ne babba da zamu yi amfani
da shi wajen kafa hujja cewa tabbas nonon
rakumi na kumshe da magani.
A bincike na kimiyya, an tabbatar da nonon
rakumi na dauke da wasu dinbin sinadirai masu
amfanar jiki kamar su Bitamin C wanda ya ninka
Bitamin C din dake a cikin nonon saniya fiye da
sau goma, sai sinadiran calcium masu karfafa
karfin kasha da hakora.
Gasu Sodium, Bitamin A da bitamin B2, sinadiran
iron, copper, magnesium, phosphorus, selenium,
potassium da dai makamantansu.
-Sinadirran dake a cikin nonon rakumi sun ba shi
damar kasancewa magani sosai dama kariya ga
wasu cututtuka inda yake karfafa garkuwar jiki.
-Yana taimaka wa wajen kaiwa da kawowar jini
a cikin jiyojin jiki.
-Yana maganin kumburin ciki dama ciwon ciki.
-Yana kare cututtukan dake yiwa ciki da hanjin
dameji.
-Yana aiki dan tabbatar da lafiyar zuciya.
-Yana maganin ciwon suga.
-Yana maganin kazzuwa.
-Yana kare koda daga kumburi ya kuma kare
mafitsara da saukaka fitar fitsari ba tsaiko.
-Yana maganin cututtukan daji kama daga
kansar mama, ciki, huhu, ko ta fata.
-Masu fama da kumburin ciki da yawan rugugin
ciki da tashin zuciya da bayan gari mai wahala
sai su rinka shan nonon rakumi.
Sai dai idan za a sha nonon rakumi to a nemi na
rakuma mai lafiya, kada a sha na rakumar da
take jinya ko take da wasu cututtukan da ana
iya daukarsu daga cikin nononta.

No comments:

Post a Comment