Friday, November 30, 2018

Maganin Ciwon Ulcer


Yan uwa masu daraja da daukaka ganin yadda
Azumi ya gabato wanda muke saran gobe ko jibi za
a tashi da shi yasa naga ya dace in dan bada
gudunmawa ga masu fama da wannan lalura don
naga wasu har ajiye Azumi sukeyi saboda wannan
lalura ina fatan Allah ya basu lafiya
Yan uwa wanda Allah ya jarabceshi da wannan
lalura yayi kokarin ya kiyaye wasu abubuwa
-shan sigari da duk wani nau'in abubuwa da suka
shafi hayaki da kan iya jawo cuta
-shan magunguna barkatai ba bisa ka'ida ba
-shan abubuwa masu yaji da zasu jawo radadin ciki
da sauran duk wani abu da kan iya jawo cutar
ABUBUWAN DA KAN TAIMAKA WAJEN MAGANCE CIWON
ULCER
-habbatus sauda'a
-hulba
-karas
-zogale
-tafarnuwa
-ayaba
-kwakwa
-zuma
-kabeji da sauran wasu abubwa da kan iya
taimakawa wajen magance cutar
MAGANIN CIWON ULCER
Wanda yake fama da wannan lalura sai ya jarabta
daya daga cikin wadannan hanyoyi insha Allahu zai
samu lafiya da yardar Ubangiji
- A samo ayaba a yayyanka a shanya a rana in ya
bushe sai a nike a rika diban garin cokali 2 a hada
da zuma cokali guda ana sha safe da yamma
- A dafa yayan hulba cokali 2 ana sha da zuma dan
kadan ko kuma a hada garin hulba ana sha da
madara safe da yamma
- A dafa ganyen zogale ana sha da Zuma safe da
yamma
- A rika cin tafarnuwa guda 3 ko 2 kullm bayan
anci sai asha ruwa Kofi guda
- A samo garin habba da hulba a had a da zuma
ana shan cokali guda da safe kafin aci komai
Muna fatan Allah s.w.t ya bamu lafiya
M.A 08

Maganin Ciwon Suga da Hawan Jini

Ko ka san cewa masana ilimin kimiyyar magunguna
na Kasar Sin da India sun tabbatar da cewar daya
daga cikin manyan magungunan warkar da ciwon
suga (diabetes) shine ganyen mangwaro?
Ganyen magwaro na dauke da sinadarai masu
yawan gaske da ke amfana wa jikin Dan’adam,
amma kash! Mutane da dama basu sani ba.
Yadda ake amfani da shi a matsayin maganin cutar
suga ( Diabetes)
(1) ka tsinko ganyan mangwaronka masu kyau sai
ka wanke su sosai
(2) Ka sanya ruwa a murhu ka tafasashi har na
tsawon minti biyar ba tare da ganyen ba.
(3) Sai a zuba ganyen a cikin ruwan zafin da ke kan
murhu tare da OLIVE oil wato man Zaitun, a barshi
yayi ta tafasa har na tsawon mintuna biyar zuwa
goma.
(4) Sai a sauke shi a tace
(5) Sai a sanya shi cikin kwano ko gilashi mai kyau
a barshi ya kwana
(6) Sai a sha wannan ruwan da sassafe bayan ka
tashi daga barci, kafin ka ci komai.
Wannan maganin, yana kawar da abubuwa marasa
kyau masu guba daga jikin mutum, kuma yana rage
yawan suga da ke cikin jini. Yana kuma saukar da
hawanjini sosai.
Haka kuma yana taimakawa matuka wajen
kwantar da tari, ASTHMA, yakan sa ka samu
numfashi mai kyau mai sauki.
Zaman dar-dar ko rashin nutsuwa sosai
(restlessness), Idan ka zuba cokali biyu ko uku a
cikin ruwan wankan ka, sannan kayi wanka dashi,
yana sanya kaji jikinka garau kuma kaji hankalin ka
ya kwanta soasai.
Dutsen dake cikin hanta ko Madata ko Koda (wato
kidney stone), mai wannan ciwon zai iya busar da
ganyen mangwaro a inuwa sannan a daka shi a
zuba garin acikin kofi/glass ko kwano a barshi ya
kwana a rinka sha kullum da safe. Wannan yana
narkar da dutsen dake jikin koda sosai.
Tari da Gushewar Murya ko Asthma ko Murya ,
A dafa ganyen Mangwaro a sanya masa Zuma
kadan yana taimakawa kwarai da gaske cikin
sauri.
> Attini ko kashi da jinni; Sai a shanya ganyen a
inuwa a busar dashi a mayar dashi gari, a rinka
sha sau uku a rana . Yana tsayar da wannan
cutar.
> Ciwon Kunne; Idan aka tatse ruwan ganyen
mangwaro aka dan dafa shi, sai a rinka digawa a
cikin kunnen. Wannan na maganin ciwon kunne.
Kunar Wuta
Sai a kona ganyen mangwaro har ya zama toka, sai
a rinka barbadawa a wurin da aka kone, yana
warkar da kunar cikin sauri zai bushe In Sha-
Allahu.
Shakuwa da ciwon makogoro
Idan kana shakuwa ko zafin makogwaro. Sai ka
kona ganyen mangwaro ka shaki hayakin, yana
maganin tsayar da shakuwan da kuma ciwon
makogwaro.
Ciwon ciki
Idan kana yawan ciwon ciki sai ka sanya ganyen
mangwaro a cikin ruwan dimi ka barshi ya kwana
sannan ka sha da safe kafin kaci komai. In ka juri
yin hakan zai warkar maka da ciwon ciki kowane
iri ne in Allah Ya yarda.
Shan ganyen mangwaro a kai a kai yana kuma kara
inganta garkuwan jiki kuma yana maganin hana
kumburin ciki. Yana da kyau ka jurewa shan
wannan ganyen mangwaro a duk safiya domin ganin
yadda suga dake cikin jikin ka zai sauka cikin sauri.
Allah (SWT) yasa mudace.

Maganin Ciwon Hanta Cikin Sauki


Ciwon hanta na daya daga cikin manyan ciwuka da
suke da wuyar magancewa a duniya amma da
Yardar Allah duk Wanda yabi abun da zamu fadi
za'a samu waraka da Yardan Allah.
ALAMUN CIWON HANTA
Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da
typhoid akai-akai,
Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki
mai tsanani,
Yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa
kasha,
Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari
ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi
,bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.
Ga duk Wanda yaji wadannan alamu sai yayi kokarin
zuwa asibiti domin Gwaji
A daina tsoron gwaji domin magance cutar tana
farkonta yafi sauki akan sanda zata tsananta.
Masu ulcer dake yawan ciwon ciki da yawan
haraswa da tashin zuciya suna magani ba sujin
sauki suyi kokarin duba lafiyar hantar su domin
takan hadu da masu ulcer sosai.
MAGANINTA
1. A samu garin habba cokali 10
2. Garin Sidir cokali 5
3. Garin tin cokali 5
4. Garin bawon kankana cokali 10
5. Garin Citta cokali 1
6. Garin tafarnuwa cokali 1
7. Garin Hidal cokali 5
8. Garin zogale cokali 3
9. Garin Yansun da raihan da kusdul hindi cokali 6
Sai a hadasu waje daya a samu Zuma lita biyu mai
kyau sai a zuba ciki a juya a hadu sosai sai a dinga
shan cokali uku sau uku a rana.
Fadakakarwa
A guji amfani da nama musamman Jan nama da
sauran abun mai ciwon hanta baya bukata.

ABUBUWAN DA AKE SO MACE TA FI MIJINTA DA SU


*Tambaya*
Aslkm, malam ya azumi dafatan kasha ruwa lafiya.
WASU TAMBAYOYI NAKE ROKON Malam daya
taimakamin da amsoshinsu in Allah yasa malam
yasansu. 1. SHIN MALAM Wai a kwai wasu abubuwa
uku da ake so mata tafi mijin da zata aura dasu,
sannan shima akwai abu guda uku da'akeso yafita
dasu?, sannan akwai wadanda sukayi musharaka
akansu, DAFATAN MALAM YASANSU KUMA ZA'A
TAIMAKAMIN DA Su. NAGODE
*Amsa*
To dan'unwa masana ilimin zamantakewar aure
suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa
uku:
1. Ta fi shi a kyau.
2. Ta fi shi kananan shekaru.
3. Ta fi son shi, sama da yadda yake sonta.
Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku:
1. Ya fi ta kudi.
2. Ya fi ta ilimi.
3. Ya fi ta jarunta.
Ana so su hadu a abubuwa uku:
1. Ya zama akwai yaran da yake hada su.
2. Ya zama addininsu daya.
3. Ya zama dukkansu suna son tarbiyya.
Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za'a samu
jin dadin aure.
*_DON NEMAN KARIN BAYANI KA NEMI SHIRIN DA NA YI A
FREEDOM RADIO RANAR: 3 GA RAMADHAN 1434 HI, A
SHIRIN NA MINBARIN MALAMAI._*
Allah ne mafi sani.

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH GUD (91)


Hadithi daga Thabitu bn Ajlan daga Alqasim bn
Muhammad daga Abu Umamah (rta) yace Manzon
Allah (saww) yana cewa :
"IDAN RANA TA FITO DAGA MAFITARTA KAMAR SIFFARTA
NA LOKACIN LA'ASAR SANDA TAKE FADUWA A
MAFADARTA, SAI MUTUM YA SALLACI RAKA'A BIYU DA
SUJADU GUDA HUDU, TO ZA'A RUBUTA MASA LADAN
WANNAN WUNIN KUMA A KANKARE MASA KUSAKURENSA
DA ZUNUBANSA. KUMA IDAN YA MUTU AWANNAN RANAR
ZAI SHIGA ALJANNAH".
ADUBA :
Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy (Juzu'i na 8 shafi
na 192).
QARIN BAYANI
***************
Wannan lokacin da ake nufi acikin wannan hadisin
shine lokacin hantsi. Domin shine ka'dai lokacin da
yayi kama da lokacin faduwar rana.
Hakika sallar walaha teana da lada mai yawa.
Manzon Allah (saww) ya fadi falalarta acikin
hadisai masu yawa.
Har ma akwai hadisin dake nuna cewa duk wanda
ya sallaci walaha ladansa kamar na wanda yayi
sadaqah ne sau 360.
Allah yasa mu dace da samun wannan babbar
falala. Ameen. Zaka iya yinta kafin ka tafi wajen
aiki ko kasuwarka. Tun daga karfe 7:30 har zuwa
11:45 duk lokacin Walaha ne. Hasali ma lokacinnata
yafi haka fa'di.
Allah yasa mu dace ameen.

RAKA'A (2) DA SUKAFI DUNIYA DA ABUN DA KE CIKINTA



ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﺭﻛﻌﺘﺎ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ
ﻭﻣﺎ ﻓﻴﻬﺎ . ‏( ﺭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ )
Manzon Allah (S.A.W) yace: Raka'o'i biyu sun fi
Duniya alkhairi da abun ke cikinta. (Muslim ne ya
rawaito)
Wace Sallace Wannan, Kuma a wana lokaci ake so
mutum yayita?
= Wannan Sallan itace Rakatayil Fajr, me raka'a
biyu, wacce ake yinta bayan futowan Alfijir, kuma
kafin a shiga Sallahn Asuba.
Ya tabbata acikin Hadisi, Manzon Allah (S.A.W) yana
karanta Fatiha ne acikin duk raka'a biyun.
Haka nan a wani Hadisin ma ya tabbatar da
Manzon Allah S.A.W ya karanta (Qul ya ayyul
kafirun a raka'an farko da Qul Huwallahu a raka'a
ta fiyu). Duk wanda mutum ya ɗauka yayi dai-dai.
GA HADISAN DA SUKA TABBATAR DA HAKAN:
1. ﻭﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ — ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ — ﻗﺎﻟﺖ: ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺨﻔﻒ ﺍﻟﺮﻛﻌﺘﻴﻦ ﺍﻟﻠﺘﻴﻦ ﻗﺒﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ ﺣﺘﻰ
ﺇﻧﻲ ﺃﻗﻮﻝ : ﺃﻗﺮﺃ ﺑﺄﻡ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ؟ ‏( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ )
2. ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ – ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ – ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺮﺃ ﻓﻰ ﺭﻛﻌﺘﻰ ﺍﻟﻔﺠﺮ: ﻗﻞ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻜﺎﻓﺮﻭﻥ، ﻗﻞ ﻫﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺣﺪ .
‏( ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ )
1. An karɓo hadisi daga Aisha Allah ya ƙara mata
yarda tace: Annabin Allah S.A.W ya kasance yana
sauƙaƙe raka'o'i biyu waɗanda suke kafin Sallahn
Asuba har sai nace: Shin kana karanta fatiha ma
kuwa? (Bukhari da Musim suka rawaito)
2. An karɓo Hadisi daga Abu Huraira Allah ya ƙara
masa yarda– Allah Annabi S.A.W ya karanta acikin
Raka'atal Fajr Qul Yaa ayyuhal kafirun, Qul
Huwallahu Ahad. (Muslim ne ya rawaito)
Ɗan uwa, Yar uwa!
Kar abarmu a baya, domin wannan wata dama ce
agaremu baki ɗaya na samun soyayyar Allah da
kuma tsira a duniya da lahira, idan muka dauwama
akan aikin alkhairi irin waɗan nan.
Manzon Allah (S.A.W yace: Mafi soyuwan ayyuka
agurin Allah, sune waɗan da aka dauwama ana
aikatasu ko da kuwa ƴan kaɗan ne.
Yaa Allah, Ka dauwamar da mu akan aikata irin
wanga ayyuka na alkhairi.

MUTANE NAU'I BIYU NE



ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺭﺟﻼﻥ: ﻋﺎﻟﻢٌ ﻭﻣﺘﻌﻠﻢٌ،
ﻭﻻ ﺧﻴﺮ ﻓﻰ ﺳﻮﺍﻫﻤﺎ . ‏( ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ )
Manzon Allah (S.A.W) yace: Mutane kala biyu ne:
Me ilimi da me neman ilimi, babu alkhairi ga waɗan
da basu ba. (Ɗabrani ne ya rawaito)
Duk mutumin da be kasance cikin jerin mutane
biyun nan ba, wato me ilimi ko kuma me neman
ilimi, to tabbas ba ze samu wannan alkhairi ba,
hasali ma shi mutacce ne. Kamar yanda Manzon
Allah ya faɗa acikin Hadisi.
Kuma ilimin da ake magana anan shine na addini.
Domin shi kaɗai ne aka wajabta mana nema wala
mace, wala namiji. Saboda da ilimin addini kaɗai
zaka san yanda zaka cika alƙawuran da ka ɗauka
ma Allah tun kana cikin mahaifiyarka cewa: Zaka
bauta ma Allah shi kaɗai, ba zaka haɗa shi da
komai ba wajen bauta. Kuma hakan ba ze yuwu ba
se da ilimi.
Amma ba wai ilim zamani ake nufi ba, wanda shima
yana da nashi amfanin sosai. Amma ka tabbata
kayi ilimin addininka kafin na zamani.
Domin duk duniya babu # jahili se wanda bashi da
ilimin addini ittifaƙan.
Ya Allah, ka bamu ilimin addininKa me amfani.
Aameen...

Abubuwa* *biyu* *basu *da* *riba.*


Abubuwa* *biyu* *basu *da*
*riba.*
1 Soyayya ba Aure
2 Aure ba soyayya
.............................
*Abubuwa biyu sukan dasa*
*kauna.*
1 Kyawawan dabi'u
2 Gaskiya
.............................
*Abubuwa biyu kan* *rusa*
*Abota.*
1 Karya
2 Gulma ko rashin yadda
..............................
*Abubuwa*
*biyu kan kara*
*kwarjini.*
1 Rukon amana
2 Ibada
..............................
*Abubuwa biyu nasa* *kunci.*
1 Cin mutuncin manya
2 Kazafi
..............................
*Abubuwa biyu nasa farin*
*ciki.*
1 Kyautatawa
2 hakuree
.............................
*Abubuwa biyu nasa*
*kusanci ga Allah.*
1 karatun qur ani
2 bin dokokinsa
.................,.............
*Abubuwa biyu nasa*
*shedan ya gujeka*
1 Ambaton Allah
2 bujirewa son xuciya
..............................
*Abubuwa biyu nasa* *ibada*
*ta karbu*
1 tauheedi
2 ikhlassi
..............................
*Abubuwa biyu da Allah*
*Yakeso*
1 Kyautatawa
2 kyakkyawan hali
......,.......................
*Abu biyune yasa na turo*
*sakonnan*
1 kasancewa musulmi
2 son da nakewa
musulunci
...........................
*Abu biyu nakeso kayi in ka*
*karanta*
1kayi aiki da shi
2 katura ma abokanka
musulmi

FA'IDODIN DAKE CIKIN YIN AURE


Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu Kididdigu ba.
Amma ga wasu ka'dan daga ciki zamu lissafo
kamar haka:
1. Yin aure biyayya ne ga umurnin Allah da
Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (saww) farin
ciki aranar lahira. Yace : "Kuyi aure ku hayayyafa.
Domin ni zanyi ma sauran al'ummomi alfahari daku
aranar Alkiyamah".
3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito ta
jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! "LA
ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI.
4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da zasu yi
maka addu'a bayan rasuwarka. Wannan yana daga
cikin ayyukan da ladansu ba zai yanke ba har
abada.
5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun
mutum daga kalle kallen Haramun, sannan ya kare
masa al'aurarsa daga Zina.
6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar taimaka ma
'Yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta
kenan daga Zina.
7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da
ninkawar ladanka fiye da wanda bashi da aure.
8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan ciyarwa da
Matarka, da daukar nauyinta, da ladan samar
mata da Mazaunin da zata rayu.
9. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Qara yawan
Musulman duniya ta hanyar haihuwar da zaka
samu.
10. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Karkatar
da himmarka daga kan neman biyan bukatarka ta
hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma
samun ladan saduwa da iyalanka.
11. Zaka samu lada mai girma sosai idan Har Allah
ya azurtaka da 'Ya'ya mata guda biyu, kumq kayi
hakuri dasu ka kyautata musu, ka kyautata
tarbiyyarsu, Su zasu zama Garkuwarka daga shiga
wuta.
12. Idan kuma har 'Ya'yanka guda biyu suka rasu,
kuma kayi hakuri, to Allah zai shigar dakai Aljannah
saboda wannan.
13. Ta dalilin aure zaka samu Qaruwar mutuncinka
da darajarka acikin al'ummah. Ka shiga sahun
mutanen da zasu iya jagorantar lamuran rayuwar
al'ummah.
14. Ta dalilin aure ne zaka Samu Taimakon Allah
cikin al'amarinka. Kamar yadda Manzon Allah
(saww) yake cewa: "MUTUM UKU, HAKKI NE AKAN
ALLAH YA TAIMAKESU
(a) WANDA ZAI YI AURE DON NUFIN KAME MUTUNCINSA.
(b). BAWA WANDA YAKE NEMAN 'YANCINSA SABODA YA
SAMU DAIDAITUWA (ACIKIN ADDINI)
(c). MUJAHIDI (MAI YAKI DON DAUKAKA ADDININ ALLAH).
15. Ta dalilin aure ne zaka samu Qaruwar yawan
dangi. Domin duk mutanen da ka auri 'yarsu ko
Qanwarsu, to ka zama nasu.
16. Ta dalilin aure ne zaka samu zuriyya tsarkaka
wadanda zasu bauta ma Allah kuma za'a baka
ladan dukkan aikin ibadar da sukayi.
* ZAUREN FIQHU yana kira ga Matasan da suke da
ikon yin aure, lallai aje ayi aure. arage burin duniya.
Kullum rayuwa tafiya take yi.

Yadda ake wankan janabaa



Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.
Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai
'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira
'siffatu kamal' (ta kamala).
Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan
kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka.
Farkon abin da zaka fara yi shi ne:
zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke
hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a
cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka، a dai-
dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka
kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda
yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi
tsarki kenan ، to daga nan kuma sai kayi alwala
irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake
a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne
wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi
shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda
biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai
ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya
bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga
jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam
yakan bude musammam gashin sa na ka, idan ka
zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai
ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a
cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka
tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata
na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka
na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka.
To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game
dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da
bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na
hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina. To idan
kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne
sai ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta
hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro.
Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba.
In wankan janaba ne haka zakayi, in na haila ne haka
za'ayi inma wanka ne na biki haka mace zata yi,
idan wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi
ma haka zaka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.
Idan mutum zai yi siffa ta 'Al ijza' wadda ta
wadatar ba sai kayi alawa acikin ta ba, kana zuwa
kayi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan
ka watsa a jikin ka ya game ko'ina, inma wani
kududdufi ne ko rami ko swimming pool sai kayi
tsalle ka fada aciki, dama ka kulla niyyar ka kafin
ka shiga, daga ka fito abin da zakayi shi ne
abubuwa guda biyu, kurkurar baki da kuma shaka
ruwa a hanci da facewa.
Shike nan, kuma ya halatta kayi sallah da wannan
wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika kamala
saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar
kamala, ya fika lada.
Kasancewar ba'ayi alwala ba ciki, wannan ka'idace
ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR)
idan sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to
da ka kawar da babban kari, karamin ma ya tafi.
Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin ace
babban ma ya tafi.
Bissalam

Bambanci Tsakanin Maniyyi, Maziyyi Da Kuma Wadiyyii


Bambanci Tsakanin Maniyyi, Maziyyi Da Kuma
Wadiyyi
...yada wannan rubutu nada muhimmanci domin
karuwar al'ummar musulmi
A kwai sakonni da dama daga 'Yan uwa da suka yi
tambaya (wata tambayar ma tafi wata guda)
akan bambancin wadannan ruwaye. Hakan ya nuna
kishinsu ga addini wanda ya sa muka yi tunanin
sanyawa a fili wadanda ba su tambaya ba ma su
amfana. Na dade ina tunanin sawa dan sauwakewa
kaina amsa tambayoyi daya bayan daya.Amma ina
jin nauyi wajen bada amsa ya sa na kasa, yau da
aka kuma yi mini tambayar na ga ya dace in sanya
tunda;
"INNALAAHA LA YASTAHYI MINAL HAQ.
Nana A'isha tana cewa:
"Allah ya jikan MATAN MADINA ko kadan KUNYA bai
taba hana su neman sanin addininsu ba" Idan muka
ce za mu ci gaba da jin nauyin tambaya ko bada
amsa saboda kunya, to zamu rayu cikin jahilci,
wanda wannan ba uzuri bane a wurin Allah.
Dan haka ga banbancin dake tsakaninsu:
{1}. MANIYYI
==========
Maniyyin namiji:- Ruwa ne mai kauri FARI wanda
yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa,
ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin
da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin
hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe
yana kamshin kwai.
{1A}. MANIYYIN MACE:- Ruwa ne TSINKAKKE, MAI
FATSI-FATSI, wani lokacin kuma yana zuwa FARI,
wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar
saduwa, ko wasa da farji.
Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa,
za ta ji tsananin sha'awa da dadi lokacin
fitowarsa. Kuma warinsa yana kama da warin
hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe
shima yana kamshin kwai. Sannan sha'awarta za
ta yanke bayan fitowarsa.
HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine:- YANA WAJABTA
WANKA.
{2}. MAZIYYI:
==========
Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar
sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce
kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin
da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin
wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya
tafiyar da sha'awa, kuma wani lokacin ba a sanin
ya fito. Malamai suna cewa:- Maziyyi ya fi fitowa
mata, fiye da maza.
HUKUNCINSA SHINE:- A WANKE FARJI GABA DAYA, DA
KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA.
{3}. WADIYYI
==========
Wani ruwa ne mai KAURI da yake fitowa a karshen
fitsari, ko kuma karshen ba haya ga wanda ya jima
bai yi jima'i ba, yana fitowa ga wadanda ba su da
aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu
ta aure, ina nufin namiji ko mace.
YANA DAUKAR HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI.
Allah shine ma sani.

Thursday, November 29, 2018

Atiku Shi Zai Dau Ragamar Nijeriya Da Zimma –Obasanjo


Tsohon Shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo
ya ce, tsohon mataimakin sa, kuma dan takaran
shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar,
zai dauki duk wani nauyi da za a dora mas da
himma.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wajen nadin
Sarautar Atiku Abubakar, a matsayin Wazirin
Adamawa, wanda Lamidon Adamawa, Dakta
Mustapha Barkindo, ya yi a fadar sa.
Ya ce, “A lokacin da muke tafiyar da al’amurran
gwamnati tare a Abuja, sam ba ya wasa da duk
wani abu da ya shafi al’ada. Kai mutum ne da
baya wasa da al’adar mutanan sa. Duk aikin da
aka dora maka a kasa ko ma a duk duniya, ina da
tabbacin z aka dauke shi ne da himma.”
A na shi jawabin, Atiku cewa ya yi, zai bayar da
mahimmanci ga sashen Masarautun mu na
gargajiya a kasar nan, ta hanyar daukaka su da
matsayin su a duniya.
Ya ce, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ciyar da
Masarautar Adamawa gaba da ma Masarautun
gargajiya na kasar nan baki-dayan su.
Atiku, wanda ya rika kiran Obasanjo a wajen
taron da shugabana, ya godewa tsohon Shugaban
kasan a bisa gudummawa da kulawan da yake yi
ma shi.
Atiku, ya nuna farin ciki da jin dadin sa da
Sarautar Waziri da aka nada ma sa, wanda hakan
yana nufin shi ne na biyu a Masarautar ta
Adamawa.
“Mai Martaba ya ba ni Sarauta mafi girman
matsayi a kan kowacce a bisa irin ci gaban da na
kawo. Marigayi Lamidon Adamawa, Aliyu
Mustapha, Allah Ya jikansa, shi ne ya nada ni a
matsayin Turakin Adamawa, a lokacin ina dan
shekaru 35, ya kuma shigar da ni a cikin ‘yan
Majalisar sa. A matsayin ka na wanda ya gaje
shi, ga shi a yau ka maishe ni mutum na biyu a
wannan Masarautar, wanda na karba tare da jin
dadi da farin ciki gami da dukkanin girmamawa a
nadin da ka yi mani a matsayin Wazirin
Adamawa.
Lamidon na Adamawa ya ce, an yi wa Atiku nadin
ne a bisa irin ci gaba da kuma gudummawar da
yake baiwa Nijeriya da kuma Masarautar ta
Adamawa musamman.
“Hakanan Atiku ya bayar da gudummawa wajen
samar da hadin kai a tsakanin al’ummar na
Adamawa, da kuma bayar da shawarwari masu
kyau ga Masarautar ta Adamawa,” in ji Lamido.
Barkindo, ya shawarci sauran masu rike da
Sarautu a Masarautar da su hada kai da sabon
Wazirin na Adamawa.
Baya ga Obasanjo, sauran manyan bakin da suka
halarci bikin nadin sun hada da, tsohon Shugaban
kasar nan, Goodluck Jonathan; Shugaban Majalisar
Dattawa, Dakta Bukola Saraki; Kakakin Majalisar
Wakilai ta kasa, Yakubu Dogara da wasu
Gwamnonin Jam’iyyar PDP da suka hada da,
Ibrahim Dankwambo (Gombe); Darius Isiaku
( Taraba); Abdufatah Ahmed ( Kwara); Seriake
Dickson (Bayelsa); Udom Emmanuel ( Akwa Ibom)
da Aminu Tambuwal (Sakkwato).
Tsaffin gwamnonin da suka halarci bikin sun hada
da, Attahiru Bafarawa na Jihar Sakkwato; Rabiu
Kwankwanso (Kano), da Boni Haruna, (Adamawa),
bikin kuma ya sami halartar ‘Yan Majalisun
tarayya na Jihohi na da, da kuma masu ci a halin
yanzun da dama.

Jam’iyyar APC Ta Dirar Wa PDP Da Atiku


Jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da sanya
siyasa a kan kashe sojojin Nijeriya daka yi a harin
da ‘yan Boko Haram suka kai garin Melete.
Jam’iyyar mai mulki ta kuma ce, zargin da
jam’iyyar adawa ke yin a cewa, an karkatar da
kudaden yaki da ta’addanci zuwa harkar yakin
neman zaben 2019, wani abu ne dake kai ga tuna
mana zamani mumamuna da jam’iyyar PDP ta yi
a lokacin tana mulki.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne a sanarwa da
jami’in watsa labaranta, Mallam Lanre Issa-
Onilu, ya raba wa manema labarai a Abuja ranar
Talata.
Sanarwar da aka raba ya nuna cewa, “Muna yin
tir da abin da muka gada daga gamnatin da ta
wuce na yadda jam’iyyar PDP ta kwashe dukkan
kudaden da aka ware don yaki da ta’adanci a
yankin arewa maso gabas.
“A bayyana yake cewa, dan takarar jam’iyyar PDP,
Alhaji Atiku Abubakar, ya shirya amfani da harkar
mutuwar sojojinmu a harin da aka kai musu a
sansanin sojoji na Metele.
“Jam’iyyar PDP da Atiku na neman siyasantar da
lamarin mutuwar ‘yan kasa da suka mutu suna
kare kasar daga ‘yan Boko Haram, abin da suka yi
rashin imani ne ga sojojin da suka mutu da kuma
iyalansu.”
APC ta kuma kara da cewa, dama haka halin
jam’iyyar PDP yake, na amfani da halin da kasa ke
ciki wajen neman farin jinin siyasa, kuma za su
girbi abin da suke shukawa lokacin zabe dake
tafe.
Sanarwa ta kuma kara da cewa, “Yan Nijeriya na
sane cewa, PDP na neman samun farin jinin da ba
su da shi ne, kuma lallai za su ji kunya nan gaba
kadan
“A yayin da jam’iyyar APC take zaman jajen
mutuwar jami’an tsaronmu da suka rasa
rayukansu a bakin aiki muna kuma ci gaba da
jinjina musu a kan aikin kare kasa da suke yi.
“Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na
nan akan bakansu na ganin an kawo karshen
wannan tashin hankalin tare da tsugunar da
wadanda aka tarwastsa sakamakon yakin.”

An Bukaci Gwamnati Ta Tallafa Wa Bangaren Ilimi


Lokaci ya yi da gwamnatocin kasar nan tare da
al’umma musamman masu hali da su kara hada
hannu wajen ganin matasa sun samu ilimi mai
kyau da inganci, kasashen da suka sai da suka
mayar da hankulan su wajen samarwa da
al’ummar su sannan suka kai halin da ake ganin
sun kai ta fannin cigaban azamani tare da bayar
da fifiko wajen samarwa matasa ilimi.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin babban
Manajan Daraktan Kamfanin sufurin motoci na AI
Gizna Global Oil and Transport Sebices Limited,
dake Kano, Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu ,
alokacin da yake zantawa da manema labarai a
Kano.Maharazu Ibrahim ya kara a cewa idon
al’ummar kasar nan musamman matasa suka
samu ilimi a su zamanto masu basira da kaifin
hankali tare kuma da tunani mai kyau da za su
zamanto abin alfahari da kawo cigaba ga
al’ummar kasa baki daya,
Manajan daraktan na AI Gizna ya nuna damuwar
shi game da yadda matasa na arewacin kasar
nan aka bar su abaya a harkokin ilimi da koyon
sana’oi, idon ka kwatanta su da matasan
kudoncin kasar nan . A cewar shi da yawa daga
cikin matasan arewacin kasar nan suna sako
sako wajen neman ilimin zamani da koyon
sana’oin dogaro da kai , wannan na daya daga cikin
yadda wasu ke amfani da su wajen tayar da
rigingimun siyasa dona addini da sauransu ,
sabodahaka ya zama wajibi al’umma su hankalta
, matukar aka baiwa matasan ilimi da sana’oi ba
za su amince wani ko wasu su yi amfani da su
ba wajen tayar da hargitsi ba .
Ganin ana kara tunkaran zabubbukan kasar nan
na 2019 ya jawo hankulan matasan da cewa ka
da su yarda a bari ayi amfani da su wajen tayar
da rigima alokacin yakin neman zabe da kuma
ranar zabe har ya zuwa ranar sanar da
sakamakon zaben shugaban kasa , gwamna, da
sauransu inji matashin dankasuwa.
Iyaye kuma su tabbatar sun rika kula da zirga
zirgan yaran su tare da sanin abokan huldarsu
da taimakawa ilimin su da tarbiyarsu da sauran
abin da ya rataya iyaye su yi wa yaran su.
A matsayin shi na manajan daraktan sufurin
motoci na AI Gizna ya yi kira ga gwamnati da ta
kara himma wajen gyara hanyoyin kasar nan da
motoci ke bi domin zirga zirga, rashin gyaran na
barazana da harkokin sufuri da wasu lokutan ke
janyo asarar rayuka da dukiyoyin masu harkar
sufuri da matafiya, amma ya ya ba da yadda
gwamnatin ke kokarin gyara wasu manyan
hanyoyin motoci na kasar nan musamman daga
Kano, Kaduna, zuwa Abuja.
Daga karshe Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu, ya
shawarci direbobin kasar nan da su guji tukin
ganganci da hakan ke jawo asarar rayuka da
dukiyoyin al’umma, sannan kuma har ila yau
direbobin su sanya tsoron Allah tare da rike
amana da masu motoci suka ba su , abin bakin
ciki ne da wasu direbobin ke aikata rashin
gaskiya da iyayen gidon su watau masu motocin
sufuri.

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga ’Yan Kungiyar Boko Haram


Na rubuto muku wannan wasika ne saboda nasan
zata isa inda ku ke, kuma sakona inada tabbacin
zai yi tasiri matuka a gurinu. Ya ku ‘yan barandan
kungiyar fafutukar kafa gwamnatin Musulunci
wannan fili mai taken HANGEN NESA yana
tattaunawa ne akan matsalolin da suka addabi
wannan kasar, musamman bangaren siyasa,
kasuwanci da kuma tsaro. Matsayina na
marubucin shafin Mailafiya, na ga ya dace in
rubuto muku wannan budaddiyar wasika, domin
in kara tunasar daku halin da hare-haren ku
yake jefa al’ummar kasar nan, da kuma yadda
kuka sanya musulmai cikin zulumi da kuma yadda
ake daukansu matsayin ‘yan ta’adda.
Ya ku ‘yan Boko Haram (kamar yadda akafi gaya
muku) kusani duk wani bincike da ilimi na
Musulunci babu inda ya ce ayi jihadi ta hanyar
kashe wadanda suka karbi addinin Allah, suna
sallah, suna azumi, suna kuma duk wata ibadar
da addini ya halasta, babu inda Allah yayi umarni
da ayi yankan rago ko kisa ga abokan zama
wadanda basu karbi sakon ba, saboda haka ne ma
ya aiko Annabawa, ya kuma sanya musu hikima
ta zance da basu littafi amatsayin wanda zai
nuna aikin da suka zo yi ban kasa, da ana kashe
al’umma hakanan, da an aiko malaku tunda wuri
sun karkashe mutanen Annabi Nuhu (A. S) amma
saboda shi Addinin Allah yana son zaman lafiya da
kwanciyar hankali, sai ya ce ayi kira zuwa addinin
gaskiya, wannan shi ne babban jihadin da Addinin
Allah ya amince, duk da ni dalibin ilimi ne, amma
kai tsaye zan iya cewa abinda ku ke ba shi ne
ainihin jihadi da Addinin Musulunci ya yi koyi ba.
Wannan kenan.
Ya ku wadannan mutane, kun yi amfani da sunan
Musulunci, kun kashe rayukan da ba za su kirgu
ba, kun kashe mutane suna Sallah, kun kashe
mutane suna tafiya zuwa guraren sana’ar su ko
makaranta, na dauka idan Addinin Allah ku ke
karewa, bazaku kashe ‘yan uwanku ahalin bautar
Allah ba, kuma Ubangijin da kuma kuka yadda
dashi, kuma ku ke da’awar yin jihadi don daukaka
Addinininsa. Shin kunada masaniyar cewar kun
maida mataye zawarawa, kun maida yara
marayu, kun maida gidaje kufe, kun sanya
hawayen mu yafara kafewa saboda yawan
zubewa da yake, kun kashe dakarun kasa dake
kare al’ummar kasa ? Don Allah wannan wace
iriyar jihadi ce ku ke yi, wace iriyar littafin Addini
ku ke karantawa wanda yake umartar ku dakuyi
wannan aikin ?
Amatsayina da dan kasa, mai kishinta da kuma
kokarin komai ya tafi daidai, ina amfani da
wannan damar da nike da ita ta isar da sako. Ina
kiranku da ku ji tsoron Allan daya halicceku, ku ji
tsoron haduwa da Ubangijin daya halicceku,
wanda zai yi hisabi akan duk ran da kuka kashe,
ku ji tausayin al’ummar da ku ke kassarawa, ku ji
tausayin musulmai da ake hantarar su saboda
ku, ana cewa su ‘yan ta’adda ne, ku yadda ayi
maslaha tare da ajje makaman ku tun kafin a
karar daku, sojojin mu masu tarin yawa da kuka
kashe, mutanen da ku ka kama ku ke azabtarwa,
‘yar uwarmu da ku ka kashe (Hauwa Liman)
kwanakin nan za su sanya gwamnati takara
daukan wasu matakan gaggawa akanku, ku ji
tsoron Allah ku fadi wadanda ke daukar
nauyinku, ku ji tsoron Allah ku tsayar da ayyukan
kashe al’umar da ba su ji ba, kuma basu ganiba,
amma kun kashe ahalinsu, danginsu kuma kun
rabasu da gidajen su da garuruwan su.
Ya ku ‘yan boko haram, mun sani cewar akwai
wasu makiyan kasa da suke amfani daku, kuma
suna daukar nauyin ku, munsan cewa kayan da ku
ke aiki dasu kuna daukan rayukan al’umma, lalle
akwai wasu ‘yan siyasa, turawa da masu kudi da
suka san wannan ta’asar da ku ke, kuma suke
temaka muku, saboda basusan kasancewar
NIJERIYA dunkulalliyar kasa, tashin hankali da
rashin zaman lafiya sune ababen sonsu, ku ji
tsoron Allah ku fallasa su. Ina kira agareku da
kuka kara karanta zancen ubangiji (Alkur’ani mai
girma ) na tabbata zaku gane cewar abinda ku
ke aikatawa yayi hannun riga da sakon Ubangiji,
na tabbata za ku yi dana sani da zubar da
hawaye bisa wannan ta’asar da kuka aikata,
kuma ku ke kan aikatawa.
Ina kara kiranku da cewar ku ajje makaman ku,
kubar wannan bakar sana’ar ta daukan rayukan
al’umma. Saboda biyayya da kauna da Addinina ya
sanya dole

Yadda matan Nigeriya Suke shan wahala a Nigeria


Wasu mata 'yan Najeriya da suka tsinci kansu a
Jamhuriyar Nijar bayan sun bar gida da zummar
tafiya kasar Saudiyya sun koka kan irin halin
ha'u'la'in da suka samu kansu a ciki.
Matan dai na yawon neman ayyukan cikin gidaje
kamar wanki da shara da sauransu, ba tare da an
biya su hakkinsu yadda ya kamata ba.
WakiliyarmuTchima Illa Issoufou ta ziyarci daya
daga cikin matan Zainab a gidan da take aiki,
wacce ta shaida mata cewa ta bar Najeriya ne
zuwa Nijar da zummar za a kai su aiki Saudiyya,
amma kuma a yanzu ba su ga tsuntsu, ba su ga
tarko.
"Na farko dai an kawo mu wajen da aka ce ta nan
ake tafiya Saudiyya, sai kuma daga bisani aka ce
mana an rufe, mu tafi idan an samu lokaci za a
daidaita komai.
"Daga baya kuma aka ce ba za a daidaita ba, kowa
ya je ya samu gidan aiki don rufawa kai asiri," in ji
Zainab.
'Mun sha bakar wahala'
Zainab ta shaida wa BBC cewa a sakamakon rashin
tudun dafawa a kasar da ba tasu ba, ya sa suka
shiga gararambar neman aiki ba dare ba rana don
tallafawa kansu.
"Mun sha wahala sosai domin kafin na samu gidan
da nake aiki yanzu, unguwa daidai ne ban sani ba a
Yamai, wata unguwar ma idan muka je sai mu
bata.
"Kuma duk yawon neman abin da za mu taimaki
kanmu muke, amma a hakan ma ba biyan bukata
yadda muke so. Wata ma sai ka gama yi mata aiki
sai ta baka abin da bai fi naira 100 ba. Wallahi har
kuka muke yi."
Asara
"Ni dai ban shirya komawa gida ba a yanzu tsakani
da Allah, saboda ba zan koma na ga takaici ba
sakamakon sayar da duk abin da na mallaka don
na yi wannan tafiya," a cewar Zainab.
Ta ci gaba da cewa a don haka ne ta dage neman
na kanta a Nijar duk da ba ta samu zuwa
Saudiyyan ba, inda aka lasa mata zuma a baki
cewar za ta mayar da abin da ta kashe a
kankanin lokaci.
"Don haka gara na zauna a nan da wuya da dadi
har na hada dan wani abin kirki."Mata na tafiye-
tafiye zuwa Saudiyya da wasu manyan kasashen
duniya ne don neman karuwar arziki a can.
Sai dai da yawansu ba sa iya cimma wannan burin
nasu, inda da dama daga cikinsu suke bigewa da
karuwanci da mu'ammali da miyagun kwayoyi da
kuma barace-barace.

Amfanin Kankana Ajikin Dan-adam


AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM
Kankana uwar ruwa tafi amfani ne a lokacin da ta
nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar
ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene
dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke
matukar taimaka ma idanu. Zakin cikinta kuma na
ba mutum karfi, tana kuma kara ma jiki ruwa.
- Nunannar kankana na taimaka ma fata saboda
sinadarin lycopene dinta.
- Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan
nitric oxide dake kara ma namiji karfin gaba.
- Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na
taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.
- Tana haifar da samuwar wadataccen barci.
- Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen
maganin cututtuka da dama.
- Tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma
ciwon koda.
- Tana da sinadarai masu kara karfin kashi (bone)
da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban
jiki (joints).

Kadan daga Cikin Amfanin Dabino a jikin 'Dan Adam


Ga wasu daga cikin amfanin dabino ga dan adam.
1. Yana samar da ruwan jiki
2. Yana taimakawa mata masu ciki
3. Yana karawa mai shayarwa ruwan nono
4. Yana gyara fatan jiki
5. Yana maganin ciwon kirji
6. Yana maganin ciwon suga
7. Yana maganin ciwon ido
8. Yana maganin ciwon hakori
9. Yana gyara mafitsara
10. Yana maganin basir
11. Yana kara lafiyar jarirai
12. Yana rage kiba, wadda ba ta lafiya ba ce
ma’ana kumburin jiki na ciwo
13. Yana maganin, majina
14. Yana sa kashin jiki ya yi karfi
15. Yana maganin gyambon ciki (Ulcer)
16. Yana kara karfi da nauyi
17. Yana maganin ciwo ko yanka
18. Yana karawa koda lafiya
19. Yana maganin tari
20. Yana maganin tsutsar ciki
21. Yana maganin kullewa ko
cushewar ciki
22. Yana rage kitse
23. Yana maganin cutar daji
(Cancer)
24. Yana maganin cutar Asma (Asthma)
25. Yana kara karfin kwakwalwa
26. Yana maganin ciwon baya,
ciwon gabbai, ciwon sanyi wanda yake kama gadon
baya.
27. Yana kara sha’awa da kuzari
28. Yana magance cututtuka dake damun kirji
29. Yana karya sihiri.

Amfanin Kunun Aya ajikin Dan-adam

Aya wacce muka sani a kasar Hausa, ana kiranta
da tigernut a harshen Turanci, Yarabawa na
kiranta da suna Ofio, a yayin da su kuma kabilar
Igbo suke kiranta da suna imumu ko aki.
Ana samun aya a sassa daban-daban a kasashen
duniya ciki har da Nijeriya.
A can baya, an dauki aya tamkar kayan kwalama
ne kawai wanda yara ke ci dan jin zaki ga bakinsu
wanda ya sa har dakuwar ayar ake yi ana
siyarwa. Wannan baya rasa nasaba da rashin
samun cikakken bayanin alfanun aya. Daga bisani
sai kimiyya ta bankado binciken wasu masana a
kan dimbin amfanin aya wanda jin haka ya sa har
kunun aya ake yi a yanzu.
Sai dai kuma har zuwa yanzu akwai mutane da
dama da ba su san amfanin shan kunun aya ba,
inda wasu sun dauka abin sha ne kawai maganin
yunwa ko kayan marmari, wasu kuma kayan zaki
suka dauke shi.
Ganin haka ya sa na zo maku da bayani tiryan-
tiryan kan aya da kuma amfaninta.
Aya tana kumshe da wasu muhimman sinadirrai
na musamman dake gina jiki, masu inganta
lafiyar jinin jiki da tsokar gangar jikin dan’adam,
masu kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin
cuta, masu maganin wasu illoli da matsalolin da
ke damun maza da mata da makamantan su.
Kadan daga cikin wadannan sinadiran sun hada da
: Phosphorus, bit E, Fat, protein, dietry fibre,
potassium, zinc, sodium, calcium, magnesium,
copper, bit C, da carbohydrates.
-An yi amanna cewa aya tana sanya jini kai wa
da karuwa a cikin kowane lungu da sako na jiyojin
jiki wanda a dalilin haka ya sa ake ganin tana
karin shawa da karfin zakari ga namiji, domin
jiyojin zakari za su rinka samun jini wadatacce
da zai rinka kai wa da kawo wa.
-Aya tana samar wa jiki da wadataccen sinadirin
bitamin E da bitamin C da kuma Zinc da sinadirin
kuercetin wanda suke da matukar amfani ga
mace ko namiji musamman masu neman
haihuwa.
-Aya tana kara yawan ruwan maniyi da kuma
lafiyarsa ga namijin da ruwan maniyinsa suka ja
baya ko yake fama da karamcin ‘ya’yan maniyi a
jiki.
-Aya tana karawa mata ni’ima, sai a nemi ayar
misalin gongonin madara daya da kuma garin
dabino rabin gongoni sai a hada da ciyawa nan da
ake kira dan hakin daka raina sai a dake a maida
ta dakuwa ko a maida su tamkar alawa a dunga
ci, kada a saka suga ko kadan.
-Aya tana kara yawan ruwan maniyi ga namiji
sai a nemi garin aya gongoni daya sai a sanya
ruwan kwakwa a dame garin a dunga sha.
-Aya na samar da yawan oestrogen wanda
karamcinsa na haifar da rashin haihuwa ga mata.
-Aya na samar da testosterone wanda shi ne
ida ya karamta ga jikin namiji to zai kasance
baya da shawa tamkar bai balaga ba, zai ga yana
ramewa kuma zakarinsa baya karuwa haka
kuma zai kasance baya da maniyi lafiyayye wanda
wannan zai hana shi haihuwa.
-Mata da kuma mazan da suke da kalubale na
rashin samun haihuwa sai su rinka amfani da aya
akai-akai.
-Aya na kara yawan ruwan nono. Dan haka ga
duk macen dake shayarwa sai ta rinka amfani da
kunun aya akai-akai bayan taci abinci.
-Mazan dake neman amfanuwa da aya sai a
zanka hada garinta dana citta a nike sai sun
koma gari sai a sanya babban cokali biyu a cikin
zuma a sha.
-Idan an ci abinci to sai a nemi kofi daya na
kunun aya a sha, hakan zai taimakawa ciki dan
saurin narkar da abinci.
-Idan aka hada garin tafarnuwa dana citta da
garin aya aka dama a tare da zuma zai bada
wasu magungunnan na daban wadanda za muyi
bayaninsu nan zuwa gaba.
-Mai fama da bayan gari mai tauri kamar na
dabbobi to sai ya rage cin shinkafa da abinci mai
karfi sai ya lazamci shan diyan itatuwa daga
bisani ya biyo baya da shan kunun aya.
-Kada a sanya suga a cikin kunun aya.
-Kada a tafasa kunun aya.
-Za a iya hada kwakwa ko dabino a madadin
suga.
Amfanin Nonon Rakumi A Cikin Dan’adam
A shekarrun baya,mutane na daukar nonon
rakumi a matsayin abinci ga diyan rakumman ko
ga masu kiwon rakumma kawai. Sannu a hankali
sai ga bincike ta bangaren magunguna sun kai ga
gano alfanun nonon rakumi.
Akwai wani lokaci a zamanin Manzon Allah
(S.A.W) da wasu mutane suka je Madina sai
rashin lafiya ta kamasu mai nasaba da
cututtukan ciki sai Manzon Allah (S.A.W) ya
umurcesu da su gauraya nonon rakumi da
fitsarinsa sannan su sha. Suna sha nan take sai
suka warke.
Wannan wani dalili ne babba da zamu yi amfani
da shi wajen kafa hujja cewa tabbas nonon
rakumi na kumshe da magani.
A bincike na kimiyya, an tabbatar da nonon
rakumi na dauke da wasu dinbin sinadirai masu
amfanar jiki kamar su Bitamin C wanda ya ninka
Bitamin C din dake a cikin nonon saniya fiye da
sau goma, sai sinadiran calcium masu karfafa
karfin kasha da hakora.
Gasu Sodium, Bitamin A da bitamin B2, sinadiran
iron, copper, magnesium, phosphorus, selenium,
potassium da dai makamantansu.
-Sinadirran dake a cikin nonon rakumi sun ba shi
damar kasancewa magani sosai dama kariya ga
wasu cututtuka inda yake karfafa garkuwar jiki.
-Yana taimaka wa wajen kaiwa da kawowar jini
a cikin jiyojin jiki.
-Yana maganin kumburin ciki dama ciwon ciki.
-Yana kare cututtukan dake yiwa ciki da hanjin
dameji.
-Yana aiki dan tabbatar da lafiyar zuciya.
-Yana maganin ciwon suga.
-Yana maganin kazzuwa.
-Yana kare koda daga kumburi ya kuma kare
mafitsara da saukaka fitar fitsari ba tsaiko.
-Yana maganin cututtukan daji kama daga
kansar mama, ciki, huhu, ko ta fata.
-Masu fama da kumburin ciki da yawan rugugin
ciki da tashin zuciya da bayan gari mai wahala
sai su rinka shan nonon rakumi.
Sai dai idan za a sha nonon rakumi to a nemi na
rakuma mai lafiya, kada a sha na rakumar da
take jinya ko take da wasu cututtukan da ana
iya daukarsu daga cikin nononta.

Siffar Mace ta Gari


Mace tagari itace wacce zata auri mutum badon
wani abu da yake dashi ba na kudi, ko mulki, ko
wata burga ta duniya masu gushewa.
A'a sai don addininsa da amanarsa kawai wanda
zaisa suyi rayuwa a duniya cikin jin dadi su mutu
su
samu aljannar ubangiji
saboda sun so juna don Allah, sunyi aure akan da'ar
Allah sannan sunyi zama irin wanda Allah yayi
umarni da ayi tsakanin ma'aurata a musulunci.
ga wasu daga cikin siffofin mace tagari
1 kiyaye lokutan ibada
2 kiyaye sirrin miji
3 juriya da haquri
4 wanka da ado
5 gyaran jiki
6 kwantarwa da miji hankali
7 kiyaye lokotan juma'i
8 gudun zargi
9 taimakawa miji
10 danne fushi
11 tarbiyantar da yaya
12 dauwama kan neman ilimin addini bisa yardan
miji.
Mace tagari bata aikata kishiyoyin abinda
ambatonsu ya gabata
haka zalika mace tagari bata..
1 bata daukaka sautinta akan na mijinta.
2 bata satar kayan abinci ko kudin miji.
3 bata saka sharadi in miji yazo zai tara da ita.
Mace tagari itace wadda aduk lokacin da miji ya
kalleta zaiji farin ciki ya lullubeshi, so da kaunarta
ya kara karuwa a cikin masarautar zuciyarsa.
Ya Allah ka hadamu da irin wadannan mata in
akwaisu a duniya albarkacin manzon tsira, Aameen
Aameen.
Tambaya:
babban abin tambaya anan shine
shin haryanzu ana samun irin wadannan kuwa ???
Wannan baya daga cikin matsalolin da malam
bahaushe ke samu kuwa ???