Thursday, December 13, 2018

YANSANDA SUNA TUHUMAR DAN MAJALISA DA LAIFIN KWARTANCI

A farkon wannan makon ne hukumar ‘yan sanda a Jihar Nasarawa ta ce ta samu nasarar kama dan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa-Eggon da Wamba da Akwanga, Abdullahi Mohammed bisa zargin yunkurin kwartanci.

‘Yan sandan sun ce sun kama shi ne lokacin yake shirin yin lalata da wata matar aure mai suna Halima Abubakar Bashir a wani otel a Abuja.

Wanda ake zargin tsohon mai taimaka wa Gwamnan Jihar Nasarawa ne a kan Harkokin Labin Shanu. ‘Yan sandan sun bayyana cewa ya nemi tursasa wa matar don ya yi lalata da ita ne saboda ya yi mata hanyar samun damar karatu a babbar jami’ar jihar da ke Keffi.

A nata bangaren, da take bayyana wa ‘yan sanda yadda lamarin ya faru, Halima Abubakar Bashir wace ke Tudun Wada a Karamar Hukumar Keffi a jihar, ta ce sun hadu da Abdullahi ne a ofishin wani jami’i a Jami’ar Keffi lokacin da suka je tare da kanen mai gidanta, don nema mata gurbin karatu.

No comments:

Post a Comment