Wednesday, December 5, 2018

HUKUNCIN FITA WAJE A GUN MATAN AURE - fita da Daya

fitan matan aure waje ba tare da
wani lalura ba haramun ne. Sai
dai idan aikin hajji za taje ko
aikin umara.
Haka kuma fitan
matan aure zuwa makaranta
haramun ne. Don Allah ya
haramta hakan a cikin suratul
nur.
Haka zuwa gidan suna ko
gidan aure ko gidan mutuwa kaf
haramun ne. Wannan shine
aqidar muslunci...
Masu aqidar cewa makarantan
matan aure ya halatta. Suna kafa
hujja ne. Da wannan hadisin na
cikin sahihul bukhari hadisin
yana cewa =
haa dasana Adam qala; haa
dasana shu'uba qala; hadasana
ibni Al-asbihan qala; yace: naji
Aba salih shine zakwan yana
zantar wa daga Abi sa'id Al-
khudri qala yace;
mata sukace da
Annabi (S.A.W) maza sun rinjayar
mana. Kai ka sanya mana wata
rana daga gareka.
Sai yayi musu
al-kawarin ranar da zai rika
haduwa dasu domin daukar ilimi
yayi musu wa'azi kuma ya
umarcesu.
Daga cikin abinda ya
gaya musu..
"BABU WATA MACE
DAGA CIKINKU DA 'YA'YANTA UKU
ZASU RIGATA GIDAN GASKIYA SAI
SUN ZAMAR MATA KATANGA DAGA
SHIGA WUTA"
sai wata mace tace;
ko biyu ma ?
Sai Annabi (S.A.W)
yace; "KO BIYU NE"
(Duba cikin sahihul bukhari littafi na uku kitabu al-ilmu babi
na talatin da biyar number na
talatin da biyar hadisi na dari da
guda daya 101)
Wannan shine hujjansu masu
cewa makarantan matan aure ya
halatta.
To anji Annabi ya
karantar da mata.
Shi Annabi ai
ma'asu mine. Baya sabon Allah.
Kuma Baya jin sha'awan mata in
ba matansa ba.
Kuma Duk matan
duniya muharramansa ne. Babu
aure a tsakaninsu.
To kai kuma
mai makarantar da matan aure baka jin sha'awane. Da
zaka tara matan mutane ka
karantar dasu.
Idan kai musulmin
gaskiya ne to ai Allah ya haramta
hakan. Dan yace idan kunga
matan da ba naku ba to ku kulle
idonku.
Duba cikin
suratul An-Nur (24) aya na talatin
da daya 31. Allah yana cewa =
Wa
qul lilmu'minaati yaghdudna min
absaarihinna wa yahfazna
furoojahunna wa laa yubdeena
zeenatahunna illaa maa zahara
minhaa walyadribna
bikhumurihinna 'alaa
juyoobihinna wa laa yubdeena
zeenatahunna illaa
libu'oolatihinna aw aabaaa'i
hinna aw aabaaa'i bu'oolati
hinna aw abnaaa'ihinaa aw
abnaaa'i bu'oolatihinnna aw
ikhwaanihinnna aw baneee
ikhwaanihinna aw banee
akhawaatihinna aw nisaaa'i
hinna aw maa malakat
aimaanuhunna awit taabi'eena
ghairi ilil irbati minar rijaali awit
tiflillazeena lam yazharoo 'alaa
'awraatin nisaaa'i wala
yadribnna bi arjulihinna min
zeenatihinn; wa toobooo ilallaahi
jammee'an aiyuhal mu'minoona
la'allakum tuflihoon =
Kacewa
muminai mata su riqa runtse
idanunsu. Su kiyaye farjojinsu.
Kada su bayyana adonsu sai dai
abin da yake a fili. Su riqa sako
mayafansu a kan rigunansu.
Kada kuma su bayyana ado sai
ga mazajensu. Har izuwa fadin
Allah ta'ala inda yace =
Kada su
riqa buga kafafuwansu don a
san irin abin daya buya na
adonsu ku tuba izuwa ga Allah
gaba dayanku. Yaku masu imani.
Ko kwa sami babban rabo)
Kaga wannan ayan ta kore
mutum musulmi yayi mu'amala
da mata. Sai dai idan matansa
ko muharramansa.
Daga cikin hujjojin mu na
haramta fitan matan aure akwai
wannan ayan
Ka duba A cikin suratul AL- AHZAB
(33) aya na talatin da uku 33. Allah
yana cewa =
Wa qarna fee bu
yoo tikunna wa laa tabarrajna
tabarrujal Jaahiliyyatil oolaa =
Kuzauna a gidajenku kada ku
dinga yin ado kuna fita kamar
yadda mutanen zamanin
jahiliyyar farko suke yi)
Wannan ayan ta haram tawa
matan aure yin yawo. Ko ina ba a
yarda ta fita ba.
Haka kuma idan aka kara duba cikin
surah al-ahzab aya na (53) Allah yana cewa =
Wa izaa sa
altumoohunna mataa'an
fas'aloohunna minw waraaa'i
hijaab; zaalikum atharu
liquloobikum wa quloobihinn; =
Idan zaku tambayesu wani abin
buqata to ku tambayesu ta bayan
tsari (wato kar kuna kallon juna)
Lallai wannan shine zaifi
tsarkakewa ga zukatanku da
zuqatansu)
Kafin in fara kawo hadisai. Duk
hadisan da zan kawo su a nan
kaje ka nemosu Zaka samu. Idan
kuma iliminka bai kai ka iya
karanta manyan littattafai ba. Irin
su sahihul bukhari da sahihul
muslim. Da abu dawda da sahihul
tirmiz ba.
To kaje ka nemi littafin =
LISSHAIKH UTHMAN ABIBAKAR
IMAM HARATI HAMDILLAH
sunan littafin BUGYATUL
MUSLIMIN WA KIFAYATUL WA

No comments:

Post a Comment