Thursday, December 6, 2018

HUKUNCIN FITA WAJE A GUN MATAN AURE- kashi na Biyu

Part 2
Haka kuma An karbo daga
Abdullahi Allah ya
yarda dashi,
daga Annabi (S.A.W) yace;
"Mace
dukkaninta tsiraici ce. Idan ta fita
waje sai shaidan ya riqa nunata.
Ma'ana sai yayi ta binta yana yi
mata wasu-wasi.
Manzon Allah (S.A.W) yace;
"Wani
namiji bazai kadaita da wata
mace ba face sai shaidan ya
zama na ukunsu" )
(Tirmizi ne ya rawaito shi)
Haka kuma Manzon Allah (S.A.W)
yace; Allah
yaji kan mutumin daya kyautata
tsakaninsa da matarsa. Lallai
Allah mai girma da daukaka ya
mallaka masa ragamarta.
Ya sanya shi ne mai kula akan
iyalinsa da ita"
Manzon Allah (S.A.W) yace;
"Kallo
kibiyace mai dafi daga kibiyoyin
iblis.
Wanda ya bar shi don tsoron
Allah Ta'ala
(wato wanda ya dai na kallon
mata dan tsoron Allah)
Allah zai bashi imani da zaiji
zakinsa a cikin zuciyarsa"
Haka kuma Dabarani ya rawaito a
cikin alqabir daga ma'akalu bin
yasar yace;
Lallai a soki dayanku
a kansa da allurar baqin karfe shi
yafi da ya shafi matar da bata
halatta gare shi ba.
Manzon Allah (S.A.W) yace;
Allah
ya la'anci mai kallo da wadda aka
kalla
Kai bama makarantan matan
aure ba. Hatta shiga a dai-daita daya
dasu ma haramun ne. Ammah
muntake wannan hukuncin kana
shiga nape da mata nima ina
shiga nape dasu. Ammah ni dan
ba yanda na iya ne.
Hujjana kuma shine
Manzon Allah (S.A.W) yace;
"Ina
tsoratar daku kadaita da mata.
Na rantse da Wanda raina yake
hannunsa.
Babu yadda za ayi
wani namiji ya kadaita da wata
mace face sai shaidan ya shiga
tsakaninsu.
Lallai mutum yayi gogayya da
aladen da yayi wanka da tabo ko
laka.
Shi yafi gare shi da yayi gogayya
da kafadar matar da bata halatta
gare shiba.
(badaruz zaujaini)
kaga kai tsaye wannan hadisin
ya haramta shiga a dai-daita da macen
da ba
matar kaba.
Wallahi Wallahi
Wallahi Bala'i ne babba Shiga a dai-daita da
mata domin kafaɗunku zai ringa
haduwa.
Haramun ne mutum ya jera da
macen da ba matarsa ba.
Ba
qanwarsa ba.
Haka hukuncin ma
yake akan mace.
Ita ma haramun
ne Ta jera da namiji. Ko ta shiga
a dai-daita
tare dashi.
Sai dai idan da lalura mai tsanani.
A aqidar musulunci
haramun ne matan aure taje
gidan biki.
Haramun ne taje
gidan suna.
Haramun ne taje
gidan mutuwa.
Saboda Annabi
muhammad (S.A.W) ya haramta
hakan a cikin ingantaccen hadisi.
Manzon Allah (S.A.W) yace;
"Mace
tsiraici ce, saboda haka ku
tsareta a gida.
Lallai mace idan ta
fita waje. Mutanen gidanta suka
ce da ita:
ina kike son zuwa ?
Sai tace zanje in gayar da marar
lafiya ko zanje wajen ta'aziyya.
To dai shaidan bazai daina binta
ba har sai ta fita daga gidan.
(wato har sai ta fita daga gidan
rasuwan da taje ta dawo gidan
ta)
To lallai mace baza ta nemi
yardar
Allah da wani abu ba.
fiye da tayi
zamanta a gidanta.
Tayi ta
bautawa Ubangijinta Tabi
mijinta)
Sayyidina Ali (R.A) Ya tambayi
matarsa fadimatu (R.A) yace
mene ne yafi alheri ga mata ?
Sai tace kada suga maza kada
maza su gansu.
Imam Ali ya kasance yana cewa:
bakwa jin kunya ?
Bakwa kishi ?
Mutum ya bar matarsa ta fita
cikin maza.
Tana kallonsu suna
kallon ta)
A'isha da Hafsatu Allah ya yarda
dasu.
Sun kasance. Wata rana a
zaune tare da Annabi (S.A.W)
sai
dan Ummu maktum ya shigo.
Shi kuma ya kasance makaho ne.
Sai Annabi (S.A.W) yace; ku tashi
ku ɓuya"
Sai suka ce ya Manzon Allah shi
wannan ba makaho bane.
Baya ganinmu kuma bai sanmu
ba ?
Sai Annabi (S.A.W) yace; To ku
makafi ne ?
Ku ba kuna ganinsa ba ?
(ABU DAWUDA DA TIRMIZI DA
NISA'I NE SUKA RAWAITO SHI)
Wannan hadisin yana nuni kan
cewa haramun ne. Suma Mata su ga
mazan da ba nasu ba. Tunda
gashi dai Annabi ya kori matansa
Sun shiga daki.

No comments:

Post a Comment