Monday, December 10, 2018

KO BUHARI BAI ISA YA HANA NI FADAR GASKIYA -DINO MALAYE

Dan majalisar dattawan Najeriya mai jawo ce-ce-ku-ce, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnati da bai dace ba.
Sanatan ya shaida wa manena labarai cewa baya tsoron tsage gaskiya a duk inda ta kama a fade ta, ba kuma ya duba daga jam'iyyar da mutum ya fito indai batun gaskiyar ya kama ko dan jam'iyyar adawa ta PDP ne, ko kuma APC mai mulki.
''Ni ba na tsoron kowa, idan akai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya."
"A halin da ake ciki ni fa ko Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko Bukola Saraki, ko Dogara kai ko uban da ya haife ni idan ya yi ba daidai ba sai na fada, babu wanda ya isa ya hana ni fadar gaskiya sai dai a kashe ni,'' inji Dino Melaye.
Sai dai har yanzu gwamnatin jihar Kogi ba ta mayar da martani ba game da batutuwan da sanatan ya zarge ta a wannan hirar ba, amma a baya ta sha musanta su.
A ranar Laraba ne rundunar `yan sandan kasar ta ayyana dan majalisar dattawan a cikin mutanen da take nema ruwa-a-jallo, bisa tuhumar da wata kotu ke masa ta taimaka wa miyagun ayyuka, zargin da ya musanta.
Haka zalika akwai kalubalen da yake fuskanta na kiranye daga al`ummar mazabarsa.

No comments:

Post a Comment